Da duminsa: An lallasa Dino Melaye a zaben fidda gwani, ya bayyana musabbabin hakan

Da duminsa: An lallasa Dino Melaye a zaben fidda gwani, ya bayyana musabbabin hakan

  • Abokin adawar Sanata Dino Malaye, Hon. Tajudeen Yusuf ya ruguza masa lissafin dawowa majalisar jiha a shekarar 2023
  • Dan siyasan ya bai wa Melaye kashi a zaben fidda gwani na kujerar sanata a PDP na yammacin Kogi da kuri'u 163
  • A martaninsa, Sanata Malaye ya taya TJ Yusuf murna, amma ya zargi cewa akwai wata kullalliyar da aka shirya mishi inda aka hade masa kai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kogi - Sanata Dino Malaye na jihar Kogi ya sha kaye a zaben fidda gwani na kujerar sanatan yammacin Kogi a jam'iyyar adawa (PDP) ga abokin adawarsa Hon. Tajudeen Yusuf.

Dino ya samu kuri'u 99, yayin da Hon. Tajudeen Yusuf, wanda a halin yanzu yake wakiltar mazabar Kabba/Bunu Ijumu, wanda ya samu kuri'u 163, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

Da duminsa: An lallasa Dino Melaye a zaben fidda gwani, ya bayyana musabbabin hakan
Da duminsa: An lallasa Dino Melaye a zaben fidda gwani, ya bayyana musabbabin hakan. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng ta tattaro yadda TJ Yusuf, wanda ya yi wakilcin majalisar dattawa so uku, ya kara da dino Malaye a daren Litinin, 23 ga watan Mayu, inda dukansu suka tashi da kuri'u 88; wanda ya yi sanadin sake zaben fidda gwanin.

Yadda TJ Yusuf ya lashe zaben fidda gwanin da a ka sake a ranar Talata, 24 ga watan Mayu, har ya kashe kusan duk kuri'un

Yayin da TJ Yusuf yake goyon bayan Nyesom Wike a jihar a matsayin 'dan takarar shugaban kasa, Dino Malaye ya goyi bayan Attiku Abubakar, hakan yasa wasan ya zama tsakanin jiga-jigai 'yan takarar shugaban kasa guda biyun masu fadi a ji na jam'iyyar.

Hakan yasa TJ Yusuf ya yi nasarar samun goyon baya daga tsagin tsohon Ibrahim Idris wanda ya samu kuri'u 72 a zaben fidda gwanin da a ka fara yi a daren Litinin.

Kara karanta wannan

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

Kuri'un Sam Aro ne suka canza bakin zaren zaben tare da taimakawa TJ Yusuf gami da dakile burin Dino Malaye na fitowa Sanata a shekarar 2023.

Dino Melaye ya yi martani

Dino Malaye ya yi martani gami da zargin "An hade masa kai".

Ba tare da kasa a guiwa ba, ya taya TJ Yusuf murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani.

Malaye ya rubuta a shafinsa na Facebook: "An yi zaben fidda gwanin kuma an yi nasara. Ina taya Hon. TJ Yusuf murna sannan ina godiya ga wadanda su ka zabe ni a karo na farko da na biyu. Hade min kai da aka yi ba ya misaltuwa, amma ina godiya ga Ubangiji. Ubangiji ya yi muku albarka baki daya. SDM"

Asali: Legit.ng

Online view pixel