Shehu Sani: Dan takarar PDP ya kwato N100m daga hannun deleget ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga
- Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda wani dan takarar kujerar majalisar wakilai a PDP ya kwato kudinsa daga hannun deleget din jam’iyyar
- Tsohon dan majalisar da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya ce dan takarar ya kwaso 'yan banga da mafarauta don karbo masa kudin da ya baiwa deleget toshiyar baki
- Ya ce dan siyasar ya kuma yi nasarar dawo da kudinsa tunda ya sha kaye a zaben fidda gwanin da aka yi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Wani dan takarar kujerar majalisar tarayya a jihar Kaduna ya yi nasarar kwato kimanin naira miliyan 100 da ya baiwa deleget din jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin toshiyar baki gabannin zaben fidda dan takarar jam’iyyar.
Tsohon sanata da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, Shehu Sani ne ya bayyana hakan a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a yammacin ranar Talata, 24 ga watan Mayu.
'Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kuɗinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin PDP
Sani ya bayyana cewa dan takarar ya kwato kudin ne bayan ya gaza samun tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwanin da aka yi, kuma ya yi amfani da 'yan banga da mafarauta ne wajen karbo kudin nasa.
Ya rubuta a shafin nasa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Wani mutum da ya rasa tikitin takarar kujerar majalisar wakilai a Kaduna ya karbo sama da naira miliyan 100 daga hannun Deleget a yammacin nan ta hanyar amfani da yan banga da maharba.”
'Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kuɗinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin PDP
A baya mun ji cewa dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Namadi Sambo, Adam Namadi ya bukaci wakilan jam’iyyar PDP da ya bai wa ko wannensu N2,000,000 su mayar masa da kudadensa da su ka tatsa kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka yi bayan ya samu kuri’u biyu kacal.
Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba
Daily Trust ta ruwaito cewa Namadi ya yi alkawarin kara wa wakilan N1,500,000 bayan an kammala zaben, sai dai shi ne ya kasance dan takarar da ya samu mafi karancin kuri’u.
Wakilan jam’iyyar sun samu miliyoyin nairori a hannun ‘yan takarar da su ka nuna matukar burin son lashe zaben fiye da abokan takararsu.
Asali: Legit.ng