Okorocha ya fallasa hikimar aiko masa EFCC ana shirin zaben ‘Dan takarar Shugaban kasa
- Sanata Rochas Okorocha ya yi magana game da durar mikiyar da jami’an EFCC suka yi a gidansa
- Tsohon gwamnan jihar Imo ya ce ana kokarin hana shi shiga zaben tsaida gwanin jam’iyyar APC
- Rochas Okorocha ya saye fam a APC, yana cikin wadanda za su nemi takarar shugaban Najeriya
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce ba a gayyace shi ofishin EFCC kafin jami’an hukumar su dura gidansa da ke birnin tarayya ba.
Premium Times ta rahoto Sanata Rochas Okorocha yana mai karyata ikirarin da hukumar EFCC ta ke yi na cewa ta gayyace shi, amma ya ki zuwa gabanta.
Rochas Okorocha ya shaidawa wasu 'yan jarida a cikin gidansa da ke Unguwar Maitama a ranar Talata cewa yunkuri ne ake yi na hana sa yin takara a 2023.
Sanatan na yammacin Imo yana cikin wadanda suka saye fam domin neman takarar kujerar shugaban kasa a APC, a makon nan ne aka fara tantance su.
A cewar Okorocha, zuwan jami’an EFCC gidansa yunkurin kawo masa cikas ne a zaben shugaban kasan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Maganar gaskiya na samu kai na a wani irin yanayi da zan iya kira tasku. ‘Yan sanda da jami’an EFCC su na gidana a yanzu".
“Da yiwuwar za su yi awon gaba da ni, kuma an rufe kofar shigowa cikin gida na.”
“Abin da na ke roko shi ne, su bar ni in je wajen tantance ‘yan takara domin ina cikin masu neman kujerar shugabancin kasa.”
“Kuma a ranar Lahadi za a shirya zabenmu (na APC). Idan ban samu zuwa wajen tantance masu takara ba, zan iya yin rashi.”
Meya kawo EFCC? - Sam Onwuemeodo
Wani Hadimin Sanatan, Sam Onwuemeodo ya tabbatarwa jaridar cewa babu dalilin da za isa jami’an EFCC su auko gidan Okorocha a rana irin jiya.
Zargin da Onwuemeodo yake yi shi ne an yi wa gidan tsohon gwamnan duran mikiya ne saboda siyasa, ganin ya na da niyyar zama shugaban Najeriya.
An nemi jin ta bakin hukumar EFCC, amma ba a iya samun mai magana da yawun na su ba.
Kan Ibo bai hadu a APC ba
Tsohon Ministan ilmin Najeriya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba ya ce har da doya aka saida domin ya iya tsayawa takara a jam’iyyar APC mai mulki.
Chukwuemeka Nwajiuba ya kuma ce Ibo sun gagara tsaida mutum daya a APC, su mara masa baya ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Asali: Legit.ng