'Dan takarar gwamna da tsohon Sakataren APC na jiha sun fice daga jam'iyyar

'Dan takarar gwamna da tsohon Sakataren APC na jiha sun fice daga jam'iyyar

  • Jigon APC, Chief Great Ogboru tare da tsohon sakataren jam'iyyar na jihar Delta sun tattara kayansu sun koma jam'iyyar APGA
  • Ɗan siyasan ya ɗauri ɗamar tarwatsa APC da raba kawunan yayanta, ya sayi Fom ɗin takarar gwamna a zaɓen 2023 karkashin APGA
  • Ogboru, shi ne ɗan siyasa lamba ɗaya da ya fi saura tsayawa neman takara a Delta tun bayan dawowar mulkin demokaradiyya a 1999

Delta - Ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Delta ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a shekarar 2015, Chief Great Ogboru, ya tattara ya fice daga jam'iyyar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ɗan siyasan ya koma jam'iyyar APGA kuma ya sayi Fom ɗin tsayawa takarar gwamna karkashin sabuwar jam'iyyar da ya koma.

Chief Great Ogboru.
'Dan takarar gwamna da tsohon Sakataren APC na jiha sun fice daga jam'iyyar Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ogboru, wanda ke matakin ɗan siyasa lamba ɗaya da ya fi fitowa neman takara a Delta tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1999, ya ɗauki ɗamarar rarraba APC.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Aisha Buhari, Ministar mata da matar mataimakin shugaban ƙasa sun dira Sakatariyar APC

A tarihin siyasarsa ya shiga jam'iyyu da dama da suka haɗa da, jam'iyyar AD, DPP da jam'iyyar Labour Party (LP) kafin daga bisani ya koma jam'iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kowace jam'iyya da ya taba zama, Fitaccen ɗan siyasan ya samu tikitin tsayawa takara amma ya ke shan ƙasa a babban zaɓe hannun ɗan takarar da PDP ta tsayar.

Tsohon sakataren APC na jihar wanda ya sauya sheka zuwa APGA tare da Ogboru a Asaba, babban birnin Delta, sun kauce wa kanfen ɗin karerayi da 'ya'yan APC ke yi kan uban gidansa.

Ya ce duk wata makarkashiya da aka shirya wa Ogboru don ɓata masa suna a idon mutane da yan takararsa na majalisar dokokin jiha ba su ci nasara ba.

A cewarsa yayin da jam'iyyar PDP ta maida hankali wajen shawo kan matsalolinta na cikin gida, ita kuwa APC, "Ta mance da kallon da ake mata ta koma kokarin bata mutum mai daraja, Ogboru."

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai, Babban jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a Zamfara, ya tsaya takara 2023

An buɗe wa ɗan takarar APC wuta a Borno

A wani labarin kuma Yan bindiga sun buɗe wa jerin gwanon motocin wani ɗan takarar APC wuta, sun halaka da dama

Wasu miyagun yan bindiga sun mamayi jerin gwanon ɗan takarar Sanata a APC, sun buɗe musu wuta da safiyar Lahadi a Borno

Rahoto ya nuna cewa yan sanda biyu sun rasa rayukan su yayin da wasu magoya baya da dama ke kwance a Asibiti sanadin harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262