Da Duminsa: Aisha Buhari da matar mataimakin shugaban ƙasa sun dira Sakatariyar APC ta ƙasa

Da Duminsa: Aisha Buhari da matar mataimakin shugaban ƙasa sun dira Sakatariyar APC ta ƙasa

  • Matar shugaban ƙasa mace lamba ɗaya, Aisha Muhammadu Buhari, da matar Obasanjo sun ziyarci Sakatariyar APC ta ƙasa
  • Manyan matan biyu tare da rakiyar Ministar harkokin matasa, Dame Pauline Tallen, sun gana da shugaban APC, Abdullahi Adamu
  • A cewar uwar gidan shugaban ƙasan sun kai ziyara ne don taya sabbin shugabannin jam'iyya murna

Abuja - Uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, Ministar harkokin mata, Dame Pauline Tallen da matar mataimakin shugaban ƙasa, Dolapo Osinbajo, sun ziyarci Sakatariyar APC ta ƙasa ranar Litinin.

Punch ta ruwaito cewa Ministar Matan ta ja hankulan manema labarai a kwanakin nan bayan ta janye daga takarar Sanata mako ɗaya bayan ta sayi Fom.

Manyan kusoshin gwamnati mata guda uku sun samu kyakkyawan tarba daga wurin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, inda suka shiga ganawar sirri.

Kara karanta wannan

Bayan kokarin sulhu, Gwamna ya shata layin yaƙi da yan bindiga, ya ce zai hana su sakat

Aisha Buhari da matar Osinbajo a Sakatariyar APC.
Da Duminsa: Aisha Buhari da matar mataimakin shugaban ƙasa sun dira Sakatariyar APC ta ƙasa Hoto: Erinjogunola Dayo Israel/facebook
Asali: Facebook

Yayin da aka jefa mata tambaya kan maƙasudin kawo ziyara, Mace lamba ɗaya a Najeriya tace sun zo ne domin taya sabbin shugabannin APC na ƙasa murna bisa samun damar jagorantar jam'iyya mai mulki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto Uwar gidan shugaban kasa ta ce:

"Mun zo nan ne domin taya shugaban jam'iyya na ƙasa murna bisa damar da Allah ya ba shi na jan ragamar wannan babbar jam'iyya, gami da gode masa kan kyakkyawan aikin da ya fara daga zuwansa."

Da take jawabi, Ministar mata ta ƙara jaddada rawar da mata zasu taka a wajen kawo muhimman cigaba da kuma manyan kujerun siyasar ƙasar nan.

Sai dai Ministan ta ƙi ta yi karin haske kan dalilin janye wa daga takarar Sanatan da ta yi burin yi ba zato ba tsammani da kuma umarnin shugaban ƙasa kan masu neman takara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da hadiminsa a mahaifar gwamnan Arewa

A ɓangaren masu adawa da suka, suna ganin cewa wannan ziyarar ta zarce ta taya murna kaɗai kasancewar sai da aka yi tafiyayya dan haɗuwa ido da ido.

Gwamnonin PDP sun shiga ganawa da Obasanjo

A wani labarin kuma Gwamnonin Jam'iyyar PDP guda Uku Sun Saka Labule da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo

Gwamnoni uku na jam'iyyar hamayya PDP sun shiga ganawar sirri da tsohon shugaban ƙasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnonin uku da suka sa labule da Obasanjo sune; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo da gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262