Ana shirye-shiryen tunkarar 2023, Tsohon Minista ya fice daga jam'iyyar APC
- Yayin da kowace jam'iyya ke shirin tunkarar 2023, tsohon ministan harkokin Neja Delta, Usani, ya sauya sheka daga APC zuwa PRP
- Jigon jam'iyyar APC na gaba-gaba a Kuros Riba ya ce ya yi haka ne domin ya cika burinsa na neman takara a zaben gwamna da ke tafe
- A watan Nuwamba 2015 shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya naɗa Fasto Udani a matsayin ministan raya Neja Delta
Cross Rivers - Jigon jam'iyyar APC a jihar Kuros Ribas, Fasto Usani Usani, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PRP, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Tsohon ministan harkokin Neja Delta ya tabbatar da batun sauya sheƙarsa a wata tattauna wa ta wayar salula da manema labarai ranar Alhamis.
Tsohuwar jam'iyyar ta shirya yin maslaha wurin tsayar da ɗan takara a zaɓen gwamnan jihar yayin da yan takara 17 ke burin karɓan tikitin na APC.
A cewar tsohon ministan:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mu muka gina jam'iyyar APC kuma mambobin APC ba abokan gaba na bane, demokaraɗiyya ta samar da yanci ga kowa."
Meyasa ya futa daga APC?
Ya ƙara da cewa ya ɗauki matakin sauya sheƙa ne domin samun cikakkiyar damar cika burinsa na zama gwamnan Kuros Riba.
Usani na ɗaya daga cikin jagorori na gaba-gaba a APC reshen Kuros Riba kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa shi a matsayin Ministan harkokin Neja Delta daga watan Nuwamba 2015 zuwa Mayu 2019.
Tsohon ministan ya nemi takarar gwamna sau uku a tarihin siyasarsa, shekarar 2003, 2011 da kuma 2019, idan ya sake tsayawa takara zai zama karo na huɗu kenan.
A wani labarin kuma Ana zabga ruwan sama, Gwanduje ya jagoranci dandazon masoya zuwa tarban Tinubu a Filin Aminu Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya jagoranci jiga- jigan APC da masoya wajen tarban Bola Tinubu a Aminu Kano.
Duk da matsanancin ruwan da aka zabga a Kano, hakan bai han a taruwar magoya baya ba a kofar shiga filin jirgin.
Asali: Legit.ng