Shirin 2023: 'Yan takara 5 na shugaban kasa a APC da ba za su da ginshikin siyasa
- Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, a hankali ana bambance aya da tsakuwa
- Guguwar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyya mai mulki ba shi ne tabbacin samun nasara ba kasancewar siyasa ta kasance wasa ce da ba ta tabbas
- A yayin da ake samun wasu ‘yan takarar da ke rike da madafun ikonsu kuma ke sa wa a rai za su gaji Buhari, wasu har a ransu sun san ba za su kai labari ba, neman suna ne kawai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Najeriya - Kamar yadda yake faruwa a kowane yanayi na siyasa a Najeriya a duk lokacin da ake gudanar da zabuka, a kullum sai an samu masu fafutukar takara da masu neman suna.
Irin wannan al’amari a halin yanzu yana kara jan hankali a jam’iyyar APC mai mulki a daidai lokacin da ake tunkarar zaben shugaban kasa na 2023.
Duk da yake akwai wadanda suke da sha'awar takara kana suke da ginshikin siyasa na gaske kuma suke ta kokarin ganin sun gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, wasu kuwa suna nan ne a matsayin cikon lamba a jerin 'yan takara.
Kamar dai yadda aka sani, Legit.ng bata yi kasa a gwiwa ba wajen tattaro muku wadannan 'yan takara. Ga su kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin 'yan takarar da sun san ba za su kai labari ba
1. Barr. (Mrs) Uju Kennedy Ohnenye
Ita ce mace daya tilo a cikin tseren takarar shugaban kasa kuma a fili bata saka takarar a rai ba.
Ohanenye ta ce adadin mazan da ke neman tsayawa takara ba zai razana ta ba, amma ba ta yi wani yunkuri na jan hankalin 'delegates' ko tuntubarsu a jihohin tarayya daban-daban ba, wanda halan barazana ce ta siyasarta.
2. Fasto Nicholas Felix Nwagbo
Shi Fasto ne dan Najeriya da ke zaune a Amurka wanda ke shugabantar Miracle Church International.
Fasto Nwagbo ya ce yana da hedikwatar cocinsa a New York, mai rassa a New Jersey, Texas Atlanta, da Najeriya. Babu wani abu da aka sani game da shi a fagen siyasa. Lamarin dai ba boyayye bane, kawai yana bata lokacinsa ne.
3. Chief Ikeobasi Mokelu
Cif Mokelu ya kasance ministan yada labarai da al'adu a zamanin gwamnatin marigayi tsohon shugaban Najeriya Janar Sani Abacha.
An ce yana da kusanci da Shugaba Buhari, amma duk da haka, ba shi da wani ginshiki na siyasa a APC. Ba kasafai ake ganinsa a bainar jama'a ba, kuma dai hakan a bayyane yake barazana ce ga takararsa.
4. Tein Jack-Rich
Jack-Rich shi ne Shugaba kuma wanda ya kafa kamfanin Belemaoil Producing Limited, kamfanin hako da habaka man fetur na farko a Najeriya.
Ya fito karara ya taka rawar gani a harkar man fetur da iskar gas amma da alama bai fahimci cewa siyasa da rigimar kasuwanci duniyoyi ne biyu da suka yi hannun riga ba.
5. Pastor Tunde Bakare
Limamin coci mai shekaru 67 da haihuwa. Ya kasance abokin takarar shugaba Buhari a zaben shugaban kasar Najeriya na 2011 karkashin rusasshiyar jam'iyyar CPC ta wancan lokacin.
Baya ga hayaniya da ake ta yadawa a kafafen yada labarai, ba a san Bakare a matsyain jigon dan jam’iyyar APC ne mai karfi ba.
Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu
A wani labarin, jigon jam'iyyar All Progressives Congress APC kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa mutum mai hikima da kwazo ake bukata matsayin shugaba ba lebura ko maji karfi ba.
A kalamansa, aikin shugaban kasa ba na hawa kan tsauni bane ko diban kankare, aikinsa tunani da amfani da kwakwalwarsa.
Yace: "Ba dan damben WWE ake bukata ba, mai tunani kan yadda za'a samar da tsaro, wanda zai yi nazari kan lamuran tattalin arziki kuma ya inganta ake bukata."
Asali: Legit.ng