Yanzu-Yanzu: Gwamna Ganduje da Sanata Barau sun dira gidan Murtala Garo don hana shi sauya sheƙa
Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, da sanatan Kano ta arewa, Barau Jibrin, sun ziyarci gidan ɗan takarar mataimakin gwamna na sulhu a APC, Murtala Garo, da tsakiyar daren da ya gabata.
Daily Nigerian ta tattaro cewa gwamna Ganduje, a wata fita ƙashin kai ba tare da jerin gwanon motoci ba ya ziyarci gida Garo da ke Railway Quarters don jawo hankalinsa kar ya bar APC.
Wata majiya da ta samu masaniya kan ziyarar ta bayyana cewa Gandune ne ya soma isa gidan Garo, kafin daga bisani Sanata Barau ya haɗe da shi a gidan.
Haka nan majiyar ta ƙara da cewa yanzu haka manyan jiga-jigan na ganawa ta sirri a gidan.
Tun a bayan dai, Garo, ya nuna damuwarsa kan matakin janye wa daga takarar Snaata da Ganduje ya yi, ya barwa Jibrin, wanda ke hamayya da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Don nuna fushinsa kan matakin da kuma gazawar gwamna wajen shawo kan tururuwar sauya sheka daga APC, Garo ya daina halartar duk wasu taruka a ciki d a wajen gidan gwamnati.
Asali: Legit.ng