Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

  • Masoyan APC a jihar Sokoto suna neman ayi zaben kato bayan kato wajen fitar da dan takarar gwamna na jam'iyyar a jihar
  • An tattaro cewa shida daga cikin manyan yan takarar jam'iyyar bakwai sun yarda da wannan tsari yayin da mutum daya ke adawa da shi
  • Sun kuma yi kira ga uwar jam'iyya da ta duba wannan bukata tasu tare da hana wasu tursasa masu karban wanda basa so

Sokoto - Magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto, a ranar Laraba, sun yanke shawarar goyon bayan tsarin kato bayan kato a zaben fidda dan takarar jam’iyyar a jihar, suna masu gargadi kan yunkurin tursasa masu wani.

Sun bayyana matsayinsu ne a wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Kwamrad Isah Jabbi, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu

Sun yi zargin cewa yan kadan daga cikin mambobin jam’iyyar na kamun kafa domin ganin an yi amfani da wakilai a zaben fidda gwanin saboda wata manufa tasu.

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben kato bayan kato
Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben kato bayan kato Hoto: APC
Asali: Twitter

Vanguard ta nakalto yana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A wannan takardar ne muke fatan kira ga shugaban kasa da mai girma Alhaji Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyarmu ta kasa da su sanya idanu a kan wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ke kokarin yin san ransu a zaben fidda gwani sabanin muradin masu rinjaye (shida cikin bakwai) na yan takarar gwamna da yawancin wakilai da magoya bayan jam’iyyar da ke so ayi zabe na kato bayan kato.
“Babban burinsu shi ne su kwace jam’iyyar su rike ta a hannunsu sannan a karshe su tursasawa magoya bayan jam’iyyar karbar dan takarar da ba sa so wanda zai iya haifar da rashin jin dadi a tsakanin masu yiwa jam’iyyar biyayya ko kuma ya sa a juyawa dan takarar jam’iyyar baya Allah ya kiyaye.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu: Majiya ta ce APC ta gama zaban wanda zai gaji Buhari a 2023

“Zuwa yanzu, mabiyan siyasar jihar sun san cewa shida daga cikin manyan ‘yan takarar gwamna bakwai na jam’iyyar APC da ke neman rike tutar jam’iyyarmu sun amince kuma sun zabi tsarin zaben fidda gwani na kato bayan kato.
“Wannan dukkan mu shaida ne cewa an sanar da majalisar zartarwar jam’iyyar APC ta kasa ta hannun shugaban jam’iyyar na kasa mai girma Alhaji Abdullahi Adamu ta wata wasika da aka fitar a ranar 17 ga Mayu, 2022."

Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya je har gida ya kai Malam Ibrahim Shekarau fam din neman takarar Sanata a NNPP.

A ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022, jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya taka har gidan Sanatan domin ba shi fam.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya

Kwankwaso ya ajiye gabar da ke tsakaninsa da Malam Shekarau bayan Sanatan na Kano ta tsakiya ya shigo jam’iyyar hamayya ta NNPP mai kayan dadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng