Ba zan fafata takara da Minista Amaechi mai murabus ba, Gwamna Badaru

Ba zan fafata takara da Minista Amaechi mai murabus ba, Gwamna Badaru

  • Gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru, ya ce ba zai iya adawa da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ba saboda ubansu ɗaya a siyasa
  • Gwamnan wanda ke neman takarar shugaban kasa karkashin inuwar APC ya ce a shirye yake ya janye wa Amaechi takara
  • Tsohon gwamnan jahar Ribas, Amaechi, ya roki Deleget na APC a Jigawa su zaɓe shi saboda ya cancanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jigawa - Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, ya faɗawa Deleget ɗin APC na jihar cewa ba zai iya fafata neman tikitin takarar shugaban ƙasa da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ba.

Da yake jawabi ga Deleget ɗin a Dutse, a gaban Amaechi, gwamnan ya ce a shirye yake ya janye wa tsohon ministan takara, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Badaru da Amaechi.
Ba zan fafata takara da Minista Amaechi mai murabus ba, Gwamna Badaru Hoto: Buharist reporters/facebook
Asali: Facebook

Badaru ya ce:

"Wasu daga cikin su zasu fara tunanin nima ina neman takara, amma ina tabbatar muku ba bu fafatawa tsakanin mu da Amaechi, haka ta faru ne saboda uban mu ɗaya a siyasa, shugaba Buhari."

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje yaƙi goyon bayan Ministan Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu duka 'ya'yan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne, wanda ya ke kaunar mu, ya girmama mu, duk abin da zamu yi yana sa mana Albarka, muna jin daɗin haka."
"Saboda haka Deleget ɗin Jigawa idan kun tuna dani ku tuna da Mista Amaechi, saboda dukkan mu ƴaƴan shugaban kasa Buhari ne. A wannan ranar ba zan iya fafata wa da shi ba."

Ku zaɓe ni saboda kwarewa ta - Amaechi

Tun da farko, Amaechi ya roki Deleget ɗin Jigawa su masa ruwan kuri'u ya samu damar ɗarewa kujerar shugaban kasa saboda cancantarsa.

Ya kulubalanci Deleget ɗin kada su zaɓe shi saboda ɗan arewa ne ko ɗan kudu sai don shi kaɗai ne ɗan takarar da ke da kwarewa a ɓangaren masu doka da masu zartarwa, a cewarsa ya fi kowa fahimtar Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun aike da sakon sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

Ya je jigawa ne bisa rakiyar manyan magoya bayansa da suka haɗa da tsohon babban hafsan sojin Najeriya, jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Tukur Buratai, tsohon Sufeta Janar, Suleiman Abba.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari zai yanke hukunci kan makomar Ministocin da suka janye takara

Babu tabbaci game da komawar Ministocin da suka janye burinsu na takara bakin aiki yayin da Lai Muhammed ya ce bai san halin da ake ciki ba.

Ministan labarai da Al'adu ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan makomar su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262