Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar
- Alhaji Atiku Abubakar ya ce wannan karon ba zai yarda a yi masa magudi kamar yadda akayi masa a 2019 ba
- Shahrarren dan siyasan yace jam'iyya mai mulki ta yi amfani da karfin ofis wajen kwace nasara hannunsa
- Jam'iyyar PDP ta dage ranar gudanar da zaben tsayar da gwanin dan takarar shugaban kasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman kujeran shugaba a 2023 karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya jaddada cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa a 2019.
Atiku yace kawai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amfani da karfin mulki wajen kwace nasarar daga hannunsa.
Ya kara da cewa sam ba zasu taba yarda a sake musu irin wannan a zaben 2023 idan jam'iyyar PDP ta bashi tikiti.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Atiku ya bayyana hakan yayinda ya hadu da deleget din jihar Kaduna a sakatariyar jam'iyyar da daren Talata, rahoton Leadership.
Ya bukaci deleget din Kaduna su kada masa kuri'a kamar yadda suka yi a zaben 2018, ya yi alkawarin ba zai basu kunya ba.
Ya tabbatar musu da cewa ba karamin taimakawa Najeriya zai yi ba idan ya zama shugaban kasa.
Yace:
"Ni na lashe zaben 2019 amma aka yi min magudi, kamar yadda aka muku magudi a Kaduna ta hanyar amfani da karfin mulki, amma ba zamu bari hakan ya sake faruwa ba a 2023."
"Saboda haka ina kira ga ku zabi shugabannin kwarai, idan na samu tikitin jam'iyyar kuma na samu nasara a 2023, zan hada kan yan Najeriya."
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, a nashi jawabin yace lallai su suka lashe zabe a 2019 amma aka hanasu.
Atiku ya lissafa jihohi 5 da yake zargin APC ta sace masa kuri’u a 2019
Legit Hausa ta zakulo jerin jihohi biyar da dan siyasar wanda ya kasance haifaffen jihar Adamawa ya zargi APC da sace masa kuri’u, ga su kamar haka:
1. Jihar Katsina
2. Jihar Kano
3. Jihar Kaduna
4. Jihar Borno
5. Jihar Yobe
Asali: Legit.ng