Jam'iyyar APC ta kammala tantance yan takaran gwamna da majalisar tarayya kusan 1,700

Jam'iyyar APC ta kammala tantance yan takaran gwamna da majalisar tarayya kusan 1,700

  • Komai ya kankama don shirin gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyya mai ci ta All Progressives Congress (APC)
  • Jam'iyyar ta kammala tantance dukkan masu takarar kujerun gwamna da majalisar dokokin tarayya
  • Yanzu yan takaran kujeran shugaban kasa ya rage jam'iyyar ta tantance

Abuja - Uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kammala tantance yan takaran kujerun siyasa a matakin tarayya da tayi ranar Lahadi, 16 ga watan Mayu, 2022.

Jam'iyyar ta tantance masu neman kujeran gwamna, yan majalisar wakilan tarayya da yan majalisan dattawa.

Tsohon hadimin Shugaba Buhari kuma mai niyyar takaran kujeran majalisar wakilan tarayya na mazabar Gaya/Ajingi/Albasu, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan.

A cewarsa, kimanin mutum 1700 da ke neman takara aka tantance cikin kwanaki biyu.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

Yace:

"Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kammala tantance yan takaran gwamna 145, yan takaran Sanata 251, da majalisar wakilai 1197 dake neman tikitin takara a zaben 2023."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC ta kammala tantance yan takaran gwamna da majalisar tarayya kusan 1,700 Hoto: @APCNigeria
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC ta rufe sayar da Fam, Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokan hamayya

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta rufe sayar da Fam din takara ga masu neman kujerar mulki karkashin lemarta a zaben kasa da za'a yi a 2023.

Jam'iyyar ta fara sayar da Fam din ne ranar 26 ga watan Afrilu, 2022.

APC ta sayar da na shugaban kasa milyan 100. A cikin kudin N30m na takarar ayyana niyya ne, N70m kuma kudin takardar neman kujeran ne.

Na gwamna kuwa, ta sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata N20m.

N10m ta sayar da Fam ga masu neman kujerar majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

Kawo ranar rufe sayar da Fam din, gwamnoni uku basu da abokan hamayya a zaben.

Sune Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum; Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahaman Abdulrazak.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng