2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara
- Wanda za a dauko a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya zama ‘dan karen aiki
- Yadda za a tsara zaben fitar da gwani ya na cigaba da kawo sabani a tsakanin shugabannin PDP
- Gwamnonin jam’iyyar PDP su na so a zabi wanda zai yi takarar shugaban Najeriya daga cikinsu
Abuja – Rahoton da ya fito daga Daily Trust a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022, ya nuna cewa ana rigima tsakanin BOT, NWC da gwamnoni a PDP.
Majalisar NWC ita ce ke rike da jam’iyya, alhakin gudanar da harkokin jam’iyya na yau da kulum ya rataya ne a kan wuyan ‘yan majalisar aiwatarwar.
Ita kuma BOT ce majalisar amintattu wanda ta kunshi dattawan da kan tsoma baki idan ta kama.
Shugabannin jam’iyyar hammayar sun yi watsi da kungiyar gwamnoni wajen zakulo wanda ake ganin ya kamata ya zama ‘dan takarar a zaben 2023.
Rahoton ya ce wannan mataki da wasu manyan na PDP suka dauka ya jawo sabani a tsakaninsu. A halin yanzu saura ‘yan kwanaki a tsaida ‘dan takara.
Tsakanin ranar 28 zuwa 29 ga watan nan na Mayu za ayi zaben tsaida gwani na shugaban kasa. Mutane 15 ne ke neman tikitin takarar shugaban kasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Za a rage yawan masu neman tuta
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa jam’iyyar na kokarin rage yawan ‘yan takarar da suka fito. Zai yi wahala a shiga zaben tsaida gwani da mutane 15.
Kamar yadda majiyar ta ce, inda matsalar ta ke shine gwamnoni sun huro wuta cewa dole a tsakaninsu za a fito da wanda zai rike tutar shugaban kasa.
Za a fasa zaben fitar da gwani a PDP?
Shugaban majalisar amintattu na PDP na kasa, Sanata Walid Jibrin yake cewa akwai yiwuwar jam’iyyar hamayyar ta fito da ‘dan takara ta hanyar maslaha.
Walid Jibrin ya shaidawa manema labarai cewa da farko an yi watsi da wannan shiri, amma yanzu akwai yiwuwar a janye matakin da aka dauka a baya.
Jibrin ya ce babu wanda za a hana takara, amma yankuna su na kokarin marawa mutum guda baya. Hakan zai sa a samu sauki wajen tsaida 'dan takaran.
A gefe guda kuma ‘yan siyasar kudancin Najeriya sun kara kaimi wajen ganin sun hana a mika takara ga ‘Dan Arewa kamar yadda aka yi a zaben da ya wuce.
APC ta na shirye-shiryenta
Dazu mu ka kawo rahoto cewa jam’iyyar APC mai mulki ta rantsar da kwamitocin da za su tantance masu neman takarar majalisar dokoki a zaben 2023.
An ba kwamitocin umarni su duba ko ‘dan takara ya biya kudin fam, kuma a binciki wadanda suka tsaya masa kafin ya samu shiga zaben na fitar da gwani.
Asali: Legit.ng