Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya

Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana burinsa na rayuwa, ya ce yana son gaje kujerar Buhari
  • Tinubu ya ce ba zai bar harkar siyasa ba har sai ya samu damar mulkar Najeriya a zaben 2023 mai zuwa
  • A bangare guda, ya ce idan aka bashi dama zai yi mulkin adalci da gaskiya a matsayinsa na shugaban kasa

Jihar Benue - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai yi ritaya daga siyasa ba har sai ya zama shugaban Najeriya.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zayyana neman kuri’un wakilan jam’iyyar a Makurdi, babban birnin jihar Benue a ranar Talata, rahoton Daily Trust.

Burin Tinubu a 2023
Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Depositphotos

A cewarsa:

“Matasan Benue ku dage don ganin an gyara muku katunan zabe. Ina tare da ku, sauran takwarorina a nan suna tare da ku da kuma sauran da dama da ba sa nan suna tare da ku don tabbatarwa da da fatan samun dunkulewar Najeriya mai albarka gare ku."

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Don haka, mun tsufa kuma idan kuna son mu yi ritaya nan ba da jimawa ba amma ba zan yi ritaya ba har sai na zama shugaban Najeriya."

Ya kara da cewa gwamnatinsa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar zai sake farfado da fatan talakawan Najeriya.

Tinubu ya kuma ce idan APC ta ba shi tikitin takara, babu sauran takara tsakaninsa da wanda zai fito a matsayin dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP.

Tinubu ya jadadda cewa zai kawo gogewar shugabancinsa a jihar Legas a matsayinsa na Gwamna da zai dace da salon shugabanci a Najeriya.

Shugaban na jam’iyyar APC na kasa ya bayar da tabbacin cewa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar zai gudanar da gwamnatin gaskiya da adalci, kamar yadda DailyPost ta ruwaito.

Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa fatattakar 'yan jarida da ya yi

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

A wani labarain, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi afuwar yan jarida a jihar Plateau kan harin da jami’an tsaro suka kai masu.

An tattaro cewa an fatattaki wasu yan jarida a yayin ziyarar da Atiku ya kai sakatariyar PDP a garin Jos a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu.

Legit Hausa ta kawo cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya isa sakatariyar ta PDP na Plateau da misalin karfe 2.19 na rana, amma da ya tarar da yan jarida suna jiransa, ya bada umurnin su fita yana cewa "ba abin da ya hada ni da yan jarida". Deleget na zo gani."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.