2023: APC ta tara sama da biliyan N29 daga siyar da fom din takara

2023: APC ta tara sama da biliyan N29 daga siyar da fom din takara

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta ci kasuwa sosai gabannin zaben fidda yan takaranta na babban zaben 2023
  • Zuwa yanzu, jam'iyyar ta tara kudi sama da naira biliyan 26 daga siyar da fom din takarar mukamai daban-daban
  • A halin da ake ciki, jam'iyyar ta kafa kwamitoci da dama da za su tantance masu neman kujerun shugabanci mabanbanta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tara kudi fiye da naira biliyan 29 daga siyar da fom din takarar kujeru daban-daban a babban zaben 2023.

Jam’iyyar mai mulki ta tsawwala fom dinta na takarar shugaban kasa zuwa naira miliyan 100, na gwamna naira miliyan 50, na sanata naira miliyan 20 sannan nay an majalisar wakilai naira miliyan 10.

Daily Trust ta rahoto cewa babban sakataren tsare-tsare na jam’iyyar ta kasa, Sulaiman Argungu, ya fada ma manema labarai a Abuja cewa yan takara 145 ne suka siyi tikitin takarar gwamna, 352 suka siya don takarar zaben fidda yan takarar sanata.

Kara karanta wannan

Orji Kalu ya ce yan takarar shugaban kasa na APC 9 na shirin janyewa, ya bayyana wanda za su marawa baya

2023: APC ta tara sama da biliyan N29 daga siyar da fom din takara
2023: APC ta tara sama da biliyan N29 daga siyar da fom din takara Hoto: APC
Asali: Twitter

Hakazalika 1,197 sun yanki fom din majalisar wakilai yayin da masu neman takarar shugaban kasa 28 ma suka yanki nasu fom din.

Jam’iyyar ta tara naira miliyan 2.8 daga siyar da fom ga yan takara 28, naira miliyan 7.2 daga yan takarar gwamna 145, naira miliyan 7 daga masu neman takarar sanata.

Sai kuma naira miliyan 11.9 daga masu neman kujerar majalisar wakiali, inda jimlar kudin ya kai sama da naira biliyan 29.

Rahoton ya nakalto Argungu yana cewa:

“Zuwa yanzu, muna da masu neman takarar gwamna 145. Mun kafa kwamitoci uku domin tantance su. Muna da masu takara 351 da suka yanki tikitin takarar sanata, yayin da muke da masu neman takarar kujerar majalisar wakilai 1,197, da kwamitoci 20. Zuwa yanzu muna da masu takarar shugaban kasa 28.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

“Kwamitocin majalisar dattawa za su kasance hudu. Bugu da kari, muna da tsare-tsaren jam’iyyarmu da za a baiwa kowani kwamiti don tantancewar, da kuma kwamitin daukaka kara. Muna kuma da tsari, na fom din tantancewa da za a baiwa kowani kwamiti.”

Ya ce an tsayar da ranar 23 ga watan Mayu domin tantance yan takarar shugaban kasa.

Orji Kalu ya ce yan takarar shugaban kasa na APC 9 na shirin janyewa, ya bayyana wanda za su marawa baya

A wani labarin kuma, shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawa, Orji Kalu, ya bayyana cewa yan takarar shugaban kasa tara daga jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) na shirin janyewa daga tseren.

Kalu wanda bai ambaci sunayen masu takarar ba, ya bayyana cewa za su marawa kudirin shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan baya, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito.

A ranar Litinin ne Kalu ya janye daga tseren neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa sannan ya nuna goyon bayansa ga Lawan.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng