Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu karon farko ya yi magana kan kalaman da ake na cewa bai da isasshen lafiya
- Tinubu wanda ke yawon yakin neman zaben delegets ya caccaki masu cewa yana fama da ciwon kafa
- Tinubu ya ce ba wai koshin lafiya kamar dan dambe ake bukata ya zama shugaban kasa ba
Minna - Jigon jam'iyyar All Progressives Congress APC kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa mutum mai hikima da kwazo ake bukata matsayin shugaba ba lebura ko maji karfi ba.
A kalamansa, aikin shugaban kasa ba na hawa kan tsauni bane ko diban kankare, aikinsa tunani da amfani da kwakwalwarsa.
Yace:
"Ba dan damben WWE ake bukata ba, mai tunani kan yadda za'a samar da tsaro, wanda zai yi nazari kan lamuran tattalin arziki kuma ya inganta ake bukata."
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Minna, yayinda ya tafi yawan kamfe wajen deleget na APC a jihar, rahoton Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon gwamnan na Legas ya bayyanawa deleget din cewa masu zaginsa bisa rashin lafiyan da yayi basu da hankali irin nasa.
Yace:
"Basu da irin kwakwalwata amma suna zagi na kullun, 'wai bai da lafiya, kafarsa na ciwo,...babu mai kwalin asibitin da nike da shi cikinsu."
"Basu da hankali ko kadan kuma basu da wani abin fadi da ya wuce zagi na amma na rabu da su."
Tinubu ya kara da cewa ya sauya fasalin jihar Legas kuma ya gyarata, haka yake son yiwa Najeriya.
Duk mu na goyon bayan Bola Tinubu a zaben Shugaban kasa – El-Rufai ya dauki matsaya
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fito karara, ya shaidawa Duniya cewa yana goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Daily Trust ta ce Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a lokacin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ‘yan gayyarsa suka kai ziyara zuwa Kaduna.
Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya ziyarci garin Kaduna a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu 2022 domin samun goyon baya a zaben fitar da gwani.
Wadanda suka yi wa Tinubu rakiya sun hada da na hannun damansa, Kashim Shettima da kuma tsohon shugaban hukumar EFCC na kasa, Nuhu Ribadu.
Asali: Legit.ng