Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa
- Abubakar Malami (SAN), Antoni-Janar kuma Ministan Shari'a na Najeriya ya janye takararsa na neman kujerar gwamnan Jihar Kebbi a zaben 2023
- Hakan na zuwa ne bayan da Malami ya ajiye aikinsa a matsayin minista kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci ministocinsa da ke da niyyar takara su yi
- Wasu majiyoyi na kusa da tsohon ministan sun ce ya fasa takarar gwamna duk da cewa hadiminsa Umar Gwandu ya ce ba a sanar da shi a hukumance ba
Abubakar Malami, Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, ya janye takararsa ta neman gadon kujerar Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, rahoton Daily Trust.
Bayan watanni ana ta hasashe, Ministan, a watan da ta gabata ya shiga takarar, yana mai neman goyon baya da al'umma.
Shugabannin jam'iyyar APC a mazaba da kananan hukumomi sun yi alkawarin goyon bayan ministan.
Jim kadan bayan ayyana takararsa, wasu na hannun daman ministan sun samu kyautan motocci daban-daban. Wasu daga cikinsu ma'aikata ne a Khadimiyya for Justice and Development Initiative, wata gidauniyya da ya kafa.
Hakan ya janyo suka da cece-kuce inda wasu ke cewa hakan wata toshiyar baki ne da Malami ya yi domin ya samu tikitin takara a jam'iyyar ta APC.
Amma, a ranar Juma'a da dare, Daily Trust ta tattaro cewa ministan, wanda ke cikin ministocin da Shugaba Buhari ya yi bankwana da su a Aso Rock tun da safe, ya janye takararsa.
Hadimin Malami ya ce ba a sanar da shi a hukumance ba
Wasu majiyoyi na kusa da ministan sun shaida wa Daily Trust cewa Malami ya janye takararsa.
Da aka tuntube shi, Umar Gwandu, hadiminsa ya ce:
"Ba a sanar da ni ba a hukumance."
Buhari ya umurci masu rike da mukaman siyasa da ke son takara a zaben 2023 su ajiye aikinsu.
2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
A wani rahoto, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng