Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara
- Kola Abiola, babban dan marigayi Cif MKO Abiola ya bayyana niyyarsa na shiga takarar shugaban kasa a 2023
- Kola ya siya fom din takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar Peoples Redemption Party, PRP ya kuma cike fom din ya mayar
- Ya yi alkawarin cewa zai yi wa jam'iyya aiki don samun nasara ko da ba shine ya ci zaben fidda gwani ba
Dan marigayi Chief MKO Abiola, wanda ake ganin shi ya lashe zaben June 12 na 1993, Kola, ya bayyana aniyarsa na yin takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam'iyyar Peoples Redemption Party, PRP.
Daily Trust ta rahoto cewa Kola ya mika fom din takararsa a sakatariyar jam'iyyar ta PRP a jiya Alhamis a Abuja.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi, Kola ya ce abin da zai fitar da Najeriya daga cikin kallubalen da ta ke fama da su a yanzu shine shugabanni na gari da ke kishin al'umma.
Ya yi alkawarin cewa duk wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar, 'duk za mu hada kai wuri guda mu yi wa jam'iyya aiki.'
A bangarensa, Sakataren jam'iyyar PRP na kasa, Babatunde Ali, ya ce jam'iyyar ta shirya tsaf domin tunkarar babban zaben na shekarar 2023.
Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan
A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.
Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.
Asali: Legit.ng