Sanin hannu: Dan takarar shugaban kasa a APC ya raba kafa, ya sayi fom din sanata

Sanin hannu: Dan takarar shugaban kasa a APC ya raba kafa, ya sayi fom din sanata

  • Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya yanke shawarar raba kafa gabanin fidda gwani da babban zaben 2023
  • Matashi kuma hazikin gwamnan wanda dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar APC, ya fara hango kujerar Sanata a jiharsa
  • Hasali ma, Ayade ya ci gaba ta hanyar saya wa kansa fom din tsayawa takarar sanata ta mazabarsa a jihar ta Kuros Riba

Kuros Riba - Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya karbi fom din takarar Sanata mai lamba 9498 a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamnan wanda ya karbi fom din sa a ranar 10 ga Mayu, 2022, zai tsaya takarar dan majalisar dattawa ta mazabar Arewa a jiharsa inda zai fafata tare da Orim Martin Ojie wanda ya karbi fom a ranar 6 ga Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Ayade ya sayi fom din takarar sanata a mazabarsu
Raba kafa: Dan takarar shugaban kasa a APC ya lallaba, ya sayi fom din sanata | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Depositphotos

Jaridar ta ruwaito cewa wasu gungun mutane da aka fi sani da ‘ya’ya maza da mata na Kuros Riba, sun saya masa fom din tsayawa takara a jam’iyyar APC domin ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamnan wanda ya bayar da tabbacin cewa zai magance matsalar rashin wutar lantarki gadan-gadan, ya ce a shirye yake ya samar da hanyar da za ta iya magance matsalar gaba daya kowa ya huta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan takarar shugaban kasa a PDP, Bala ya lallaba ya sayi fom din gwamna

Ba Ayade kadai ba, yayin da Bala Mohammed ke cikin jerin 'yan takarar shugaban kasa na PDP, a boye ya lallaba ya sayi fom din takarar komawa kujerar gwamnan jihar Bauchi a wa'adi na biyu, kamar yadda Premium Times ta ce ta samo.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

Gwamna Mohammed dai zai cika wa'adinsa na farko a matsayin gwamnan jihar Bauchi ne a 2023, kuma zai iya sake neman takarar gwamnan a karo na biyu.

An sha hasashe kan wanda zai gaje shi a 2023 bayan da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a kwana nan.

Daya daga cikin irin wadannan hasashe ya nuna cewa sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya shiga wata yarjejeniya da gwamnan domin ya zama mai rike masa da mukaminsa.

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin kuma, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.