Sanatan Kebbi ta tsakiya: Alaka ta yi tsami tsakanin Aliero da Gwamna Bagudu kan wanda zai mallaki tikitin APC
- Siyasar APC a Kebbi na kara zafi kan wanda zai mallaki tikitin jam’iyyar na sanata mai wakiltan jihar ta tsakiya
- Ana fafutukar tikitin ne tsakanin Sanata Adamu Aliero wanda shine a kan kujerar a yanzu da Gwamna Atiku Bagudu wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu
- Rikicinsu ya samo asali ne tun bayan da aka sauke mambobin jam’iyyar masu biyayya ga Aliero daga shugabancin jam’iyyar a jihar
Kebbi - Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kebbi kan kudirin Gwamna Abubakar Bagudu na son zama sanata.
Gwamnan wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a watan Mayun 2023, yana neman tikitin jam’iyyar na sanata mai wakiltan yankin Kebbi ta tsakiya, Daily Trust ta rahoto.
Sanata Adamu Aliero ne a kan kujerar a yanzu haka kuma yana neman zarcewa a karkashin inuwar jam’iyyar ta APC.
Alaka ta yi tsami a tsakanin Aleiro da Bagudu tun bayan tarukan jam’iyyar mai mulki a jihar. Shugabannin biyu na fafatawa kan wanda zai ja ragamar tsarin jam’iyyar.
Dan majalisar ya koka kan tursasa yan takara a yayin taronsu da tsige mambobin jam’iyyar da ake ganin suna biyayya gare shi a tsarin shugabannin jam’iyyar.
Da yake magana a yayin gangamin siyasa a watan Janairu, Aliero ya ce rikicin siyasa na jiran APC a jihar idan jam’iyyar ta ki yin adalci a tsakanin mambobinta.
Ya ce:
“Za a samu mummunan sakamako idan APC a jihar Kebbi ta kasa yin adalci ga kowa. A yayin babban taron jam’iyyar da ya gabata an cire wasu ‘ya’yan jam’iyyar a matsayin shugabanni saboda son rai yayin da aka daura wasu a kan mukamansu. Ba za mu bari hakan ya kasance ba kuma ba za mu lamunci hakan ba.”
Masu sa ido kan harkokin siyasa a jihar sun ce gwamnan jihar yana da damar lashe tikitin takarar Sanata na jam'iyyar.
APC ta sake kara wa'adin sayar da foma-foman takara
A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar APC ta sake tsawaita wa'adin sayar da fom din takara da sauran shagulgulan da ta sa a gaba gabanin babban zaben 2023.
Wannan sauyi na zuwa ne daidai lokacin da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka fara mayar da cikakkun foma-foman takara ga jam'iyyar a makon nan.
APC ta kara wa'adin sayar da fom din daga ranar 10 ga watan Mayu zuwa Alhamis, 12 ga watan Mayu, yayin da ta dage mayar da foma-fomai zuwa gobe Juma'a, 13 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng