Tsohon Sakataren Gwamnati ya hango matsala, yace da yiwuwar a fasa zaben Shugaban kasa
- Samuel Oluyemisi Falae ya na ganin zai yi wahala INEC ta iya shirya zabe da kyau a shekarar badi
- Cif Olu Falae ya ce a halin yanzu abubuwa sun tabarbare a Najeriya, babu zaman lafiya a ko ina
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya yace idan aka tafi a haka, ba zai yiwu a zabi shugabanni ba
Ondo - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Olu Falae ya na da ra’ayin cewa halin da ake ciki a Najeriya ya yi tabarbarewar da zai iya kawo cikas a 2023.
A wata hira ta musamman da aka yi da Cif Olu Falae a jaridar Punch, tsohon mai shekara 83 ya nuna cewa watakila zaben shekara mai zuwa ba zai yiwu ba.
Tsohon Ministan tattalin arzikin yake cewa a yadda ake tafiya, an fara hangen yiwuwar hakan.
Falae yake cewa yanzu rayuwa ta zama babu tabbas, ana iya kashe mutum farat daya. Tsohon ya ce ba zai so ya zauna a Najeriya alhali ana wannan ta’adi ba.
Tsoron da nake ji kenan - Falae
“Abin da nake tsoro ya tabbata. Ina tsoron kasar ta rincabe. Rincabewa ita ce a shiga halin da doka da tsari zai daina aiki a a kan kowa, a ko ina, ko yaushe.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kamar yadda masanin siyasar nan, Thomas Hobbes yake cewa mutum ya zama dodo ga ‘danuwansa, kowa na ta kansa, Allah ne ya rage ga kowa.”
“Idan ka fi makwabacinka karfi, sai ka karbe masa dukiya da matarsa, da duka abin da ka ke so a wurinsa, ka kashe, kayi duk abin da kake so, shikenan.”
“Mun fara hangen zuwan wannan lokaci da abin da yake faruwa a nan a shekaru bakwai, takwas, tara, goma da suka wuce. Tsoro na kar kasa ta rincabe.”
Zaben 2023 zai yiwu kuwa?
“Ina da matukar shakku sosai a kan yiwuwar 2023. Meyasa? Bayan rikici da kashe-kashe da ake yi, INEC ta fada cewa an kashe mata daruruwan jami’ai.”
“An lalata wasu daga cikin kayan aikinsu, an kona ofisoshi da motocinsu. Saura shekara daya ayi zabe, amma ana yi wa INEC da ma’aikatanta wannan aiki.”
“Me zai faru kenan tsakanin yau zuwa lokacin zabe. Ba na tunanin za ayi wani zabe mai ma’ana a 2023, domin rashin tsaro yana neman kai intaha a kasa.”
Me zai faru kenan? Ba za a iya yin zabe ba, kuma wa’adin masu mulki a jihohi da tarayya zai cika. Ba za a iya canzar gurabensu ba saboda barna ta shigo.”
Osinbajo zai kai labari
A gefe guda akwai masu ganin za ayi zabe a 2023, har an ji labari, Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo yana sa ran zai lashe zaben fitar da gwani a APC
Mai ba Shugaban kasa shawara a kan harkar iyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya ce alamu sun nuna masu cewa lallai Farfesa Osinbajo ya kama hanyar samun nasara.
Asali: Legit.ng