2023: Jerin ministocin da suka yi murabus bayan umurnin Shugaba Buhari

2023: Jerin ministocin da suka yi murabus bayan umurnin Shugaba Buhari

Abuja A ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ministocinsa da suka ayyana aniyarsu ta yin takarar shugaban kasa da sauran kujeru a 2023 da su yi murabus daga mukamansu.

Shugaban kasar ya bayyana a taron majalisar zartarwa cewa ministocin da sauran mambobin majalisarsa da ke son takarar mukamai a 2023 su yi murabus zuwa ranar Litinin, 16 ga watan Maris.

2023: Jerin ministocin da suka yi murabus bayan umurnin Shugaba Buhari
2023: Jerin ministocin da suka yi murabus bayan umurnin Shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Zuwa yanzu, akalla ministoci uku da ke hararar kujerar shugaban kasa a 2023 ne suka cika umurnin. Sune:

Emeka Nwajiuba

Emeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi ya yi murabus daga majalisar shugaban kasa Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sanar da batun murabus dinsa a yayin zaman majalisar zartarwa a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, kuma babban hadimin shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

A cewar ministan, ya bar majalisar ne domin ya mayar da hankali kan kudirinsa na son zama shugaban kasa da zaben fidda gwani na APC mai zuwa.

Godswill Akpabio

Ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus.

Mataimakin ministan na musamman, Jackson Udom, ya tabbatar da murabus din nasa.

Akpabio na daya daga cikin ministocin shugaban kasa Buhari da ke son su gaje shi a zabe mai zuwa.

Ogbonnaya Onu

Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu ya yi murabus.

Ministan ya mika takardar murabus din nasa a ofishin sakataren gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu.

Majiyoyi a ofishin sakataren gwamnatin sun bayyana cewa sun karbi takardar ajiye aikin da ministan ya gabatar bayan umurnin shugaban kasar a majalisar zartarwa ta tarayya.

2023: Ministan Buhari ya bayyana abun da zai yi kafin ya bi umurninsa na yin murabus

A wani labarin, ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr Chris Ngige, ya bayyana cewa zai tuntubi shugaban kasa Muhammadu Buhari da al'ummar mazabarsa kafin ya yi murabus daga matsayinsa a majalisar zartarwa ta kasar.

Kara karanta wannan

Da dumi: Malami, Amaechi da sauran Ministocin Buhari dake neman takara sun yi murabus

Ministan na martani ne ga umurnin da shugaban kasa Buhari ya bayar a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, cewa dukka mambobin majalisarsa da ke hararar kujerun siyasa a 2023, su yi murabus kafin ranar 16 ga watan Mayun 2022, Leadership ta rahoto.

Ngige, wanda ya yi magana bayan taron majalisar zartarwa a Abuja a ranar Laraba, ya kara da cewar shugaban kasar ya bayar da wata kafa da duk wanda ke neman karin bayani a kan furucinsa zai tuntube shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng