Umarnin Buhari: Ministan Buhari ya shiga takara, ya yi murabus daga mukaminsa
- Bayan umarnin shugaban kasa, ministan Buhari ya hakura, ya ajiye aiki zai kuma mai da hankali kan takara
- A yau ne Buhari ya umarci mukarrabansa da su yi murabus idan za su ci gaba da yin takara a zaben 2023
- An samu wasu na kusa da shugaban da suka bayyana aniyar tsayawa takarar kujeru daban-daban a zaben 2023 mai zuwa
Abuja - Ministan harkokin Neja Delta Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban a yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na ranar Laraba ya umurci dukkan mambobin majalisar ministocinsa da ke hangen ofisoshin a zaben mai zuwa da su yi murabus kafin ranar 16 ga Mayu.
A wata tattaunawa da jaridar The Nation, mai taimaka wa Ministan kan harkokin yada labarai, Jackson Udom, ya tabbatar da murabus din mai gidan nasa.
Ya ce:
“Ministan ya yi murabus. Ya mika takardar murabus dinsa ga SGF. Muna jiransa a ICC, inda zai zo ya mika fom din tsayawa takara.”
Sai dai Udom bai bayyana ranar da shugaban nasa ya mika takardar murabus dinsa ba, kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito.
Bayanin hakan na zuwa ne a matsayin martani ga rahotannin da ke cewa Akpabio ya janye daga takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Udom ya kara da cewa masu yada karya su daina, domin Akpabio na a cikin takara daram a jam'iyyar APC mai mulki.
Tinubu ya bayyana abin da zai yi idan ya fadi zaben fidda gwani na APC
A wani labarin, Asiwaju Bola Tinubu, daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki ya magantu kan abin da zai yi idan ya fadi a zaben fidda gwani da jam'iyyar ta shirya yi.
Bayanan na Tinubu na zuwa ne jim kadan bayan da rahotanni suka yadu kan cike ka'ida da ya yi kana da mayar da fom din takarar APC ga shugabannin jam'iyyar.
Ya kuma tabbatar wa mabiyansa cewa zai yi nasara. Sai dai ya ce idan ya sha kashi, zai amince da shan kaye ba tare da wani kurnu ba. Tsohon gwamnan jihar Legas a cikin bidiyon ya fadi cikin harshen Yarbanci cewa:
Asali: Legit.ng