Ci gaba: Tsohon shugaban kasa Jonathan ya samu sabon babban mukami a duniya
- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai bi sahun tsohon firaministan kasar Birtaniya, Mr. Tony Blair a matsayin mamba a kwamitin kula da harkokin kasashen Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya (ECAM Council)
- Jonathan ya zama shugaba na farko a Afirka da ya samu irin wannan nasarar ganin yadda kungiyar ta yi masa tayin nada shi babban matsayi
- An kafa ECAM tare da manufar habaka gaskiya, inganci, da mafita mai dorewa ta fannin tsarin kiwon lafiya mai dorewa
Biyo bayan rahotanni game da aniyar takarar shugaban kasa na Goodluck Jonathan, dan siyasar ya samu babban mukami na mamba a kwamitin ba da shawara na kasa da kasa na kungiyar Tarayyar Turai kan Nahiyar Afirka da Gabas ta Tsakiya (ECAM Council).
Kamar yadda PM News ta ruwaito, Jonathan ya zama shugaba na farko a yankin hamadar Sahara da ya zama shugaban hukumar ECAM ta kasa da kasa.
ECAM kungiya ce mai zaman kanta da aka kafa tare da manufar ingantawa da bunkasa dangantaka tsakanin kasashen Turai, Afirka, da MENA ( Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka), tare da Italiya da ke taka muhimmiyar rawa a ciki.
Jonathan ya shiga sahu da tsohon Firayim Ministan Burtaniya, Tony Blair a matsayin mamban kwamitin
Kungiyar tana alfahari da gama manyan mambobi kamar tsohon Firayim Ministan Burtaniya, Tony Blair, tsohon shugaban Hukumar Tarayyar Turai, José Manuel Barroso, da sauran wasu jiga-jigai da dama.
Kamar yadda takardar nadin nasa ke kunshe dashi, shugaban hukumar ta ECAM Dr. Kamel Ghribi ya ce hukumar za ta yi farin cikin tarbar tsohon shugaban kasa Jonathan zuwa ofishinsa, kmar yadda Independent ta ruwaito.
Bayan kus-kus da dare, an gano dalilin ganawar shugaban APC da Jonathan
A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a daren ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, abin da ke tabbatar da abin jita-jita game da sauya shekar Jonathan zuwa jam’iyya mai mulki.
Ganawar ta ranar Litinin ta zo ne sa’o’i uku bayan da wata kungiyar Fulani makiyaya ta biya Naira miliyan 100 domin karbar fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ga Jonathan.
A cewar jaridar Leadership, ainihin dalilin da ya sa jiga-jigan biyu suka gana shi ne don tattaunawa kan muradin Jonathan na komawa shugabancin kasar nan a 2023.
Asali: Legit.ng