Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takarar kujerar Sanata

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takarar kujerar Sanata

  • Ganduje ya shiga jerin gwamnonin dake neman komawa majalisa bayan karewar wa'adinsu a 2023
  • Ganduje zai yi takara da Sanata Barau Jibrin a zaben tsayar da gwanin da za'a yi makonni masu zuwa
  • Gwamnan na Kano ya zabi mataimakinsa Gawuna ya gajesa, kuma kwamishanan Garo matsayin mataimakinsa

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi Fom din takarar kujerar Sanata na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Dan siyasan mai shekaru 72 a duniya na shirin wakiltar mazabar Kano ta Arewa a majalisar dattawan tarayya.

Ganduje, zai kara da Sanata Barau Jibrin wanda ke rike da kujeran tsawon shekaru bakwai yanzu.

Ganduje ya rike matsayin mataimakin gwamna karkashin Rabiu Kwankwaso 1999-2003 sannan suka sake tafiya tare 2011-2015.

Ya gaji maigidansa na lokacin inda ya lashe zaben gwamnan jihar a 2015 kuma ya sake cin zabe a 2019.

Kara karanta wannan

Billahil lazi la ilaha illahuwa za mu rike maka amanarka – Gawuna ga Ganduje

Idan ya kammala wa'adinsa a 2023, yana niyyar cigaba da kasancewa a gwamnati.

Abdullahi Ganduje
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata Hoto: @thecable
Asali: Twitter

2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yana so mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, ya gaje sa ne saboda biyayyarsa.

Daily Trust ta rahoto yadda gwamnan da wasu shugabannin jam’iyyar suka tsayar da Gawuna domin ya mallaki tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC sannan suka lallashi kwamishinan karamar hukuma, Murtala Sule-Garo ya hakura ya zama abokin takararsa.

An gabatar da hukuncin a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ranar Talata sannan aka amince da shi gaba daya.

Sai dai gwamnan ya shaidawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kano a ranar Talata cewa ya yanke kan Gawuna ne bayan kammala tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda ya kara da cewa, an bi dukkan ka’idojin jam’iyyar kafin cimma matsayar.

Kara karanta wannan

Na samawa matasa 700 aiki a jihar Kebbi, na sama wa mutum 6000 tallafin Korona: Abubakar Malami

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng