Yau ake yin ta a PDP, za a dauki mataki a kan wadanda za a ba tikitin Shugaban kasa

Yau ake yin ta a PDP, za a dauki mataki a kan wadanda za a ba tikitin Shugaban kasa

  • Majalisar kolin jam’iyyar PDP za ta yi wani zama na musamman a babban ofishinta da ke Abuja
  • A wannan zaman NEC na 97, za a amince da maganar yankin da za a ba takarar shugaban kasa
  • Haka zalika majalisar za ta yanke shawara a kan wurin da yadda za a shirya zaben tsaida gwani

Abuja - Idan ba a samu wata matsala ba, a yau Laraba, 11 ga watan Mayu 2022, jam’iyyar hamayya ta PDP za ta yi zaman babbar majalisar koli watau NEC.

Jaridar Daily Trust tace za ayi wannan taro da aka dade ana jira ne hedikwatar PDP da ke Abuja.

Batutuwan da za a tattauna a kan su a wajen wannan taro sun kunshi rahoton kwamitin mutum 37 da ya yi aiki a kan yankin da ya dace a mikawa takara.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Zaman NEC din da za ayi yau shi ne zai zama na 97 tun da aka kafa PDP a 1998. A taron za a amince da wurin da za a shirya zaben tsaida ‘dan takara.

Majalisar kolin ta NEC ce ta ke da wuka da nama domin daukar matsaya a kan batun inda PDP za ta tsaida ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Sauya-shekar Goodluck Jonathan

Wata majiya ta ce majalisar za ta tattauna a kan zawarcin da jam’iyyar APC mai mulki ta dade ta na yi wa tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Neman Shugaban kasa
Nyesom Wike a Katsina Hoto: @officialpdpnig
Asali: Facebook

Zargin kusancin Goodluck Ebele Jonathan da jam’iyyar APC ya yi karfi, har ta kai an samu wasu da suka saya masa fam din neman takarar shugaban kasa.

Kafin yanzu, rahoton ya ce ana ta samun sabani tsakanin majalisar aiwatarwa ta NWC da majalisar amintattu ta BOT a kan maganar wanda zai rike tutar PDP.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

An ki daukar matsaya har yanzu

Wani jagora a jam’iyyar adawar ya shaidawa manema labarai cewa babu wani sabon abu a kan maganar ware takara domin PDP ta saida fam ne ga kowa.

‘Yan siyasar Kudu da Arewa duk sun saye fam din shiga takarar shugaban kasa wannan karo a PDP, ya ce hakan ta sa jam’iyyar APC ta gaza daukar matsaya.

The Guardian ta ce akwai yiwuwar NEC ta amince da shawarar da ake zargin kwamitin Samuel Ortom ya bada na barin kowa ya nemi takara a zaben 2023.

An tuntubi sakataren yada labaran PDP, Debo Ologunagba, amma ya ce a saurari zaman na an jima.

Masu shirin takara a PDP

Kun samu labari an tantance masu neman takara PDP irinsu Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Bala Mohammed, Aminu Tambuwal, Peter Obi da Nyesom Wike.

Sauran masu hangen takarar shugaban kasa 2023 PDP, sun hada da; Mohammed Hayatu-Deen, Anyim Pius Anyim, Udom Emmanuel da kuma Ayodele Fayose.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnati ya hango matsala, yace da yiwuwar a fasa zaben Shugaban kasa

Sai kuma irinsu; Nwachukwu Anakwenze, Dele Momodu, Sam Ohuabunwa, Cosmos Ndukwe, Charles Ugwu, Chikwendu Kalu, da Misis Oliver Tareila Diana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng