Jam'iyyar APC ta rufe sayar da Fam, Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokan hamayya

Jam'iyyar APC ta rufe sayar da Fam, Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokan hamayya

  • Jam'iyyar All Progressive Congress APC ta rufe sayar da Fam din takara karkashin a zaben 2023.
  • Kawo yau da aka rufe sayar da Fam, Farfesa Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokan hamayya
  • Jam'iyyar ta APC ta saki sabon ranakun da take son duk wanda ya sayi Fam ya dawo da shi

Wuse, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta rufe sayar da Fam din takara ga masu neman kujerar mulki karkashin lemarta a zaben kasa da za'a yi a 2023.

Jam'iyyar ta fara sayar da Fam din ne ranar 26 ga watan Afrilu, 2022.

APC ta sayar da na shugaban kasa milyan 100. A cikin kudin N30m na takarar ayyana niyya ne, N70m kuma kudin takardar neman kujeran ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Na gwamna kuwa, ta sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata N20m.

N10m ta sayar da Fam ga masu neman kujerar majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.

Kawo ranar rufe sayar da Fam din, gwamnoni uku basu da abokan hamayya a zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sune Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum; Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahaman Abdulrazak.

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC ta rufe sayar da Fam, Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokin hamayya

APC ta saki sabon ranakun da take son duk wanda ya sayi Fam ya dawo da shi

A sabon jadawalin da jam'iyyar ta saki da daren Litnin, ta umurci dukkan wadanda suka karbi Fam su cike kuma su dawo da shi ranar Laraba, 11 ga Mayu, 2022.

Bayan haka ranar Juma'a za'a fara tantance Gwamnoni, yan majalisar wakilai, Sanatoci da shugaban kasa ranar Asabar, 14 ga Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Adamu Garba ya ce ya janye daga takara karkashin APC

Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adamu Garba, ya janye daga takarar saboda wasu dalilai.

A jawabin da ya saki a shafinsa ranar Talata a Abuja, Garba yace ya janye daga takarar ne saboda tsadar Fom din APC da kuma tsadar yin kamfe.

A cewarsa, sayar da Fam N100m zai maishe da siyasar Najeriya wajen cin kasuwa ne kawai ba shugabancin kwarai ba.

Yace ya yanke shawarar janyewa bayan shawara da kwamitin kamfensa kuma kawo yanzu sun samu N83.2 million sakamakon gudunmuwa daga wajen masoya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng