Zan Kafa Makarantar 'APC' Idan Aka Zaɓe Ni a 2023, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Fayemi
- Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce zai kafa makaranta ta jam'iyyar APC idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023
- Fayemi, wanda ya furta hakan a yayin wani taro da ya kira a Abuja ya ce makarantar za ta rika bawa shugabanni horaswa ne kan jagoranci da mulki
- Ya kara da cewa zai yi aiki tare da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, da kakakin majalisar jihohi don warware matsalolin Najeriya
FCT, Abuja - Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti, ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa, zai kafa makaranta ta All Progressive Congress, APC, domin bawa shugabanni horaswa, rahoton The Cable.
Gwamnan na Ekiti na daga cikin wadanda ke neman gadon kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a jam'iyyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da ya ke jawabi wurin wani taron cigaban ƙasa da ya kira a ranar Litinin a Abuja, Fayemi ya ce za kuma a yi amfani da makarantar wurin rantsar wa da bawa shugabannin APC horaswa.
"Zaburar da shugabannin jam'iyyar mu zai kunshi saka ido sosai kan shirye-shirye da tsare-tsaren mu," in ji shi.
"Don haka, zan tabbatar cewa kowanne shekara, jam'iyyar mu ta kira taro don bita kan cigaba da muka samu wurin aiwatar da ayyukan mu da sake duba dabarun mu bisa sabon yanayi.
"Aikin kafa makaranta na jam'iyyar APC zai samu kulawa a karkashin jagoranci na domin za a yi amfani da shi wurin rantsar da horas da jami'an mu, da ba su koyarwa a shugabanci da mulki."
Dan takarar shugabancin kasar ya ce zai yi aiki da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, don magance kalubalen da ke addabar kasar.
Ya kuma ce zai yi aiki tare da kakakin majalisar jihohi don daidaito wurin samun nasarorin magance matsalolin kasar.
2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng