Daruruwan mambobin APC da PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP a Kaduna
- Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙara karfi a jihar Kaduna yayin da take shirin tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe
- Mambobin manyan jam'iyyu APC da PDP mutum 1,000 sun sauya sheka zuwa NNPP a wani yankin jihar ta Kaduna
- A cewar ma su sauya shekan, sun ɗauki matakin ne duba da kyakkyawan manufar jam'iyyar ga yan kasa da matasa
Kaduna - Jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari reshen jihar Kaduna ta karbi sabbin mambobi daga wasu jam'iyyu a Hayin Banki, ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa.
Jaridar Aminiya ta rahoto cewa mambobin manyan jam'iyyu biyu, APC da PDP guda 1000 ne suka bi sahun Kwankwaso, suka sauya sheƙa zuwa NNPP.
Bayanai sun nuna cewa jam'iyyar ta shirya taro na musamman domin tarban dandazon masu sauya shekar a Anguwar Hayin Banki dake Kaduna.
A jawabinsa na wurin taron, shugaban NNPP na mazaɓun Hayin Banki, Anguwar Kanawa da Farin Gida, ya bayyana cewa jam'iyyar su ta maida hankali ne wajen ceto yan Najeriya daga halin da suka tsinci kan su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa mutanen Najeriya sun sha baƙar wahala a hannun manyan jam'iyyun APC da PDP, bisa haka ne NNPP ta zo domin sanya farin ciki da annashuwa a zuƙatan yan Najeriya.
Meyasa suka ɗauki matakin komawa NNPP?
Ɗaya daga cikin masu sauya sheƙa kuma ɗan takarar majalisar dokokin jiha mai wakiltar Kawo, Hassan Usman Goma, ya ce sun yanke komawa NNPP ne saboda kyakkyawan kudirinta ga yan Najeriya musamman matasa.
Manya-manyan jiga-jigan NNPP sun samu damar halartar taron, daga cikin su har da masu neman takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Daga ciki har da ɗan takarar majalisar wakilan tarayya, Muhammad Ali, ɗan takarar majalisar dokokin jiha, Magaji Ɗanladi, da sakataren NNPP na jihar Kaduna, Manjo Yahaya mai ritaya.
A wani labarin na daban kuma Ministan Man Fetur da wani gwamnan APC sun karɓi Fom, sun shiga takarar shugaban ƙasa a 2023
Ƙaramin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva, ya ayyana shiga jerin masu neman gaje kujerar Buhari karkashin APC a 2023
Kungiyar magoya baya da fatan Alheri ta lale miliyan N100m ta siyawa Ministan Fom kuma ta gabatar masa da shi. Haka nan kuma Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya karɓi Fom ɗin tsayawa takara daga wurin masoyansa.
Asali: Legit.ng