Da Duminsa: Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya shiga takarar shugaban ƙasa a APC

Da Duminsa: Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya shiga takarar shugaban ƙasa a APC

  • Ƙaramin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva, ya ayyana shiga jerin masu neman gaje kujerar Buhari karkashin APC a 2023
  • Kungiyar magoya baya da fatan Alheri ta lale miliyan N100m ta siyawa Ministan Fom kuma ta gabatar masa da shi
  • Haka nan kuma Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya karɓi Fom ɗin tsayawa takara daga wurin masoyansa

Abuja - TVC News ta rahoto cewa ƙaramin ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya ayyana kudirinsa na shiga tseren takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Tuni dai kungiyoyin magoya baya suka gabatar masa da Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa na Miliyan N100m a APC.

Gwamna Ayade da Ministan Fetur Sylva.
Da Duminsa: Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya shiga takarar shugaban ƙasa a APC Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Haka zalika ƙungiyoyin sun gabatar wa gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba Fom ɗin takara. Tun a baya dai gwamnan ya ayyana shiga takara bayan gana wa da Buhari a Villa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Mutanen biyu sun zama mambobin APC na baya-bayan nan da ɗumbin magoyan su suka karɓan musu Fom din Miliyan N100m a madadin su, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun a watan Afrilu, gwamna Ayade ya ayyana shiga takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya, inda ya ce ya yi haka ne bayan amincewar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan karban Fom ɗin a Abuja, Gwamna Ayade ya ce ya yi an gani a jihar Kuros Riba kuma zai iya mafiyin haka a matakin ƙasa.

Siyan Fom ɗin takara miliyan N100m

Farashin Fom ɗin takara na jam'iyyar APC miliyan N100m ya jawo cece kuce tsakanin yan Najeriya.

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, na ɗaya daga cikin manyan mutanen da suka lale miliyan N100m suka Sayi Fom.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Sauran wasu daga ciki sun hada da jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emeliefe.

A wani labarin kuma Babban Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga mukaminsa, ya sayi Fam ɗin fafatawa a 2023

Hadimin gwamnan jihar Ekiti kan harkokin kwadugo, Oluyemi Esan, ya yi murabus daga kan kujerarsa

Mista Esan ya ɗauki wannan matakin ne domin ya samu damar neman takarar ɗan majalisar wakilai a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262