2023: Fasto Tunde Bakare ya ayyana neman takarar kujerar Buhari a hukumance
- Gabannin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar APC, adadin masu son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari na karuwa
- A yau Litinin, 9 ga watan Mayu, Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son shiga tseren shugaban kasa karkashin jam'iyya mai mulki a hukumance
- Tsohon abokin takarar shugaban kasar a zaben 2011, ya dauki alkawarin kawo sauyi a kasar tare da dinke baraka
Abuja - Shugaban Cocin Citadel Global Community a Najeriya, Tunde Bakare, ya ayyana aniyarsa ta shiga tseren kujerar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.
A wani gagarumin biki da aka yi a cibiyartaro ta Musa Yar’Adua da ke Abuja, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, faston ya yi alkawarin shugabanci mai kyau a kasar, Nigerian Tribune ta rahoto.
Hakazalika, Bakare wanda ya kasance tsohon abokin takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a rusasshiyar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) a zaben 2011 ya ba dukkanin yan Najeriya tabbacin samun cikakken tsaro idan har ya zaman shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Bakare ya yi alkawarin yin adalci ga Najeriya ta bangaren zamantakewa da tattalin arziki, ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba.
Vanguard ta rahoto cewa dan takarar shugaban kasar ya nuna jajircewarsa wajen cimma sabuwar Najeriya inda ya yi alkawarin dinke Baraka tsakanin baya, yanzu da na gaba.
Ya ce:
“Ina mai gabatar da kaina a matsayin gada tsakanin Najeriyar yau da wacce za ta zo a gaba.”
2023: Tsohon Abokin Takarar Buhari Ya Lale N100m Ya Siya Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC
A baya mun kawo cewa Tunde Bakare, a ranar Alhamis, ya siya fom din sha'awa da takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC gabanin zaben 2023 a Abuja, Vanguard ta rahoto.
Hakazalila, Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie, ta sanar da siyan fom din takarar na Bakare cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar 5 ga watan Mayu.
A cikin rubutun da ke hade da hoto, an hangi Fasto Bakare a hoton rike da fom din takarar da ya siya kan Naira miliyan 100 na jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriya.
Asali: Legit.ng