Yadda Gwamnonin APC 3, SGF da wasu jiga-jigai suka hana Yari da Marafa komawa PDP
- Akwai yiwuwar APC ta iya rasa Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba Marafa a jihar Zamfara
- Alamu na nuna tsohon gwamnan Zamfara Yari da kuma Sanata Marafa sun kama hanyar barin APC
- Tun da Bello Matawalle ya dawo jam’iyyar APC daga PDP ake samun sabani saboda rabon mukamai
Zamfara - Wani rahoto da ya fito daga Daily Trust a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu 2022, ya yi karin haske kan rikicin da APC ke fama da shi a jihar Zamfara.
Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba Marafa su na cikin tsaka mai wuya, domin an hana su sauya-sheka daga jam’iyyar ta APC.
Jaridar ta ce ana samun wani sabon rashin jituwa a APC ne bayan Bello Matawalle ya shigo jam’iyyar.
An rasa yadda za ayi rabon mukaman jam’iyya na SWC tsakanin manyan jagororin APC irinsu Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa da mutanen Gwamna.
Wani ‘dan jam’iyyar ta APC ya shaidawa jaridar cewa tun da mutanen Yari da Marafa suka rasa mukamai a jihar Zamfara, suka shiga shirin sauya-sheka.
Yari ya je, ya dawo?
Abdulaziz Yari wanda ya yi gwamna tsakanin 2011 da 2019 ya kama hanyar ficewa daga APC, amma ya hakura saboda neman takarar shugaban jam’iyya.
Bayan ya gagara zama shugaban APC na kasa, Yari ya sake dawo da maganar barin jam’iyyar.
Manya sun sa baki
Hakan ya jawo aka shiga yin zaman sulhu da gwamnonin APC, Kayode Fayemi (Ekiti), Nasiru El-Rufai (Kaduna) da Mohammad Badaru Abubakar (Jigawa).
Wadannan gwamnoni uku da ake ji da su a jam’iyyar APC sun yi kokarin shawo kan barakar da ake samu a jihar Zamfara domin gudun a samu cikas a 2023.
Baya ga sa-bakin gwamnonin, majiyar ta ce sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya na bakin kokarinsa na ganin ya dakatar da shirin sauya-shekar.
Yari da Marafa za su rabu
Alamu na nuna cewa watakila Yari ya yi zamansa a APC saboda kasuwancinsa da kuma shari’a da yake fuskanta a kotu, amma da wahala Marafa bai tashi ba.
Marafa na iya shiga wata jam’iyyar adawa, domin ya nemi kujerar gwamna a Zamfara a zaben 2023. Idan aka cigaba da tafiya a hakan, lokaci zai iya kure masu.
Ba mu koma PDP ba tukun - Marafa
A baya an ji labari Kabiru Marafa ya shaidawa Duniya cewa zuwa yanzu bai shiga jam’iyyar adawa ta PDP ba, amma ya tabbatar da cewa ya na shirin hakan.
Tsohon Sanatan na jihar Zamfara ya ce labarin da yake yawo na sauya-shekarsa ba gaskiya ba ne, duk su na kan zama da jagororin PDP, NNPP da jam'iyyar Accord.
Asali: Legit.ng