Wata Ministar Buhari Ta Ayyana Niyarta Na Yin Takara a Zaɓen 2023
- Dame Pauline Tallen, Ministan Harkokin Mata da Ayyukan Cigaba, ta ayyana niyarta na yin takara a 2023
- Tallen za ta yi takarar kujerar sanata ne na Plateau North inda ake sa ran za ta fafata da Simon Lalong wanda shima ana ganin zai nemi kujerar
- Farfesa Nora Dadu'ut, sanata mai rike da kujerar a halin yanzu ba za ta sake yin takara ba a 2023 hakan ya bawa Tallen damar shiga takarar
Ministan Harkokin Mata da Ayyukan Cigaba, Dame Pauline Tallen, ta ayyana niyarta na yin takarar kujerar sanata a mazabar Plateau South a babban zaben 2023, rahoton Daily Trust.
Shigar Tallen takarar ya kara yawan ministocin Shugaba Muhammadu Buhari da suke hararren kujerun siyasa daban-daban a shekarar 2023.
Tallen za ta fafata da Simon Lalong
Ministan za ta fafata da Gwamna Simon Lalong da shima ake kyautata zaton yana da niyyar yi takarar kujerar. Lalong ya kammala wa'adinsa biyu a matsayin gwamnan Plateau.
Mazabar Plateau South ta kunshi kananan hukumomi guda shi da suka hada da Langtang North, Langtang South, Mikang, Qua’anpan, Shendam, da Wase.
Rahotanni sun ce sanatan da ke kan kujerar yanzu, Farfesa Nora Dadu'ut ba za ta sake yin takarar kujerar ba a 2023, hakan ya bawa ministan damar ta nemi takarar.
A baya,Tallen ta taba rike mukamin kansila, kwamishina da kuma mataimakiyar gwamna.
2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng