Shugaban INEC ya musanta raɗe-raɗin yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Shugaban INEC ya musanta raɗe-raɗin yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

  • Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ya musanta rahoton cewa zai iya neman gaje Buhari a zaɓen 2023
  • A wata sanarwa da Sakataren watsa labaransa, Rotimi Oyekanmi, ya fitar, Yakubu ya ce hakan ba zata taɓa faruwa ba
  • A cewar sanarwan, Yakubu ya maida hankali wajen aiwatar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe ba tare da banbanta yan takara ba

Abuja - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya musanta rahoton dake yawo cewa da yuwuwar ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ƙungiyar marubutan ƙare haƙƙin ɗan adam ta Najeriya, a ranar Lahadi, ta yi kira ga yan Najeriya ka da su kaɗu idan suka ga shugaban INEC ya sayi Fom ɗin APC miliyan N100m.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ƙungiyar ta yi wannan tunani ne bayan ganin an saya wa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara a APC.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.
Shugaban INEC ya musanta raɗe-raɗin yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Amma da yake martani ta hannun Sakataren watsa labaransa, Rotimi Oyekanmi, ranar Lahadi, shugaban INEC ya bayyana cewa ba shi da sha'awar shiga tseren takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.

A sanarwar da sakataren ya fitar don musanta jita-jitar mai taken, "Kiran da ake shugaban INEC ya shiga tseren takara a 2023," Yakubu ya ce hakan ba zai taɓa yuwuwa ba.

Leadership ta rahoto Wani sashin sanarwan ya ce:

"An ja hankalin mu kan wasu karerayi da ake yaɗawa a wani ɓangaren Najeriya cewa ka da mutane su yi mamaki idan suka wayi gari shugaban INEC ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa ko rokon ya shiga."
"Wannan ikirarin ya zarce hankali, ba zai taɓa faruwa ba. Shugaban hukumar zaɓe ya maida hankali wajen gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Yakubu ya maida hankali kan sauke nauyi da aka ɗora masa - INEC

Sanarwan ta ƙara da cewa nauyin da kundin mulki ya ɗora masa na shugaban zaɓe kuma baturen zaɓen shugaban ƙasa ya ishe shi kuma nan ya maida hankalinsa.

"Shugaban hukuma zai cigaba da kokarin sauke nauyin dake kansa ba tare da nuna goyon baya ko tsanar kowace jam'iyyar siyasa ko ɗan takara ba."

A wani labarin kuma Saboda Tsadar kuɗin Fom, Tsohon shugaban APC ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

Shugaban APC na farko tun bayan kafa jam'iyyar a Neja, Alhaji Bako Shettima, ya tattara kayansa ya yi murabus daga cikinta.

Shettima wanda ke neman takarar gwamnan a Neja, ya ce jam'iyyar ta cika kudin Fom kuma hakan ya nuna ba dan mutane aka kafa ta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel