Da duminsa: Yankin Yarbawa sun hada kai, sun yanke dan takaran APC da za su zaba
- Shugabannin jam'iyyar APC a Kudu masio Yamma sun cimma yarjejeniya da masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
- A cewar Cif Bisi Akande, ‘yan takarar sun yi alkawarin tattaunawa da kansu da kuma jama’a don haifar da da mai ido
- Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu; Sanata Ibikunle Amosun da dai sauransu
Legas - Bayan ganawar da ’yan takarar shugaban kasa a shiyyar Kudu maso Yamma da shugabannin jam’iyyar APC suka yi, rahotanni sun ce ‘yan takarar sun amince cewa yankin ya fitar da dan takarar jam’iyyar APC na gaba.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande, ya fitar a karshen wata ganawa da ‘yan takarar shugaban kasa na shiyyar a daren Juma’a a jihar Legas.
A cewarsa, ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ta Kudu maso Yamma, gwamnoni da sauran shugabanni sun hada kai ne kafin zaben 2023 don tsaida batu daya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A Akande:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Muna da hadin kai ta yadda za mu tabbatar da cewa Shugabancin Tarayyar Najeriya zai zo Kudu maso Yamma.
“Mun yi tattaunawa mai amfani. Mun kuma yanke shawarar cewa kowa ya kiyaye cikakkiyar akidarsa saboda muna da hadin kai."
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu; Sanata Ibikunle Amosun da Kakakin Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila.
Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai
Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ido hudu da maigidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas.
Manyan jigogin APCn biyu sun hadu ne a taron zaman hadin kai tsakanin yan takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC daga yankin kabilar Yoruba.
Dattawan yankin kudu maso yamma ne suka shirya zaman don ganin yadda za'a hada kai da juna don tsayar da mutum guda cikinsu.
Dattawan sun hada da tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande, da tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba.
Wadanda ke hallare a zaman sun hada da Jigon APC Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi, da Ministar harkokin cikin gida Rauf Aregbesola.
Shirin 2023: Tsohon gwamnan Zamfara Yarima ya bayyana aniyarsa ta gaje Buhari
A wani labarin, jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan Zamfara Sanata Ahmed Yerima ya shiga tseren takarar shugaban kasa na 2023.
Yerima, wanda ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa guda uku da suka hada da rashin tsaro, talauci da jahilci.
Yerima, wanda ya dauki hankulan al’ummar kasar nan a lokacin da ya kawo shari’a jihar Zamfara a matsayin Gwamna, ya kuma ce nan take zai sayi fom din tsayawa takara da kuma nuna sha’awa a jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng