Shirin 2023: Tsohon gwamnan Zamfara Yarima ya bayyana aniyarsa ta gaje Buhari
- A ranar Juma'a ne tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya
- Ya bayyana haka ne a Abuja, inda yace zai tsayi fom tare da bayyana aniyarsa ta gaje Buhari a hukumance
- Yeriman Bakura ya kuma bayyana mabufofinsa uku da yake son cimmawa idan ya zama shugaba a 2023
Abuja - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan Zamfara Sanata Ahmed Yerima ya shiga tseren takarar shugaban kasa na 2023.
Yerima, wanda ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa guda uku da suka hada da rashin tsaro, talauci da jahilci.
Yerima, wanda ya dauki hankulan al’ummar kasar nan a lokacin da ya kawo shari’a jihar Zamfara a matsayin Gwamna, ya kuma ce nan take zai sayi fom din tsayawa takara da kuma nuna sha’awa a jam’iyyar APC.
Jaridar Daily Trust ta tattaro Yerima na cewa::
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na zo nan da yammacin yau ne domin in sanar da shugaban kasa aniyar shiga takarar zaben 2023 da kuma tsayawa takarar ofishin shugaban Tarayyar Najeriya. Zan sayi fom dina yau insha Allahu in bayyana aniyata yau da yamma a hukumance.
“Don haka, ni ma ina da manufofi uku; yaki da rashin tsaro, yaki da talauci, da jahilci."
Shugaban APC da ya gina jam'iyyar a Neja ya fice daga cikin jam'iyyar mai mulki
A wani labarin, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC tun farkon kafa ta reshen jihar Neja, Alhaji Bako Shettima, ya fice daga jam'iyya mai mulki.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon jigo a APC ya bayyana dalilinsa na ɗaukar wannan matakin da wasu abubuwa da ake yi a jam'iyyar da suka sha ƙarfinsa.
Shettima wanda ke fafutukar zama gwamnan Neja ya sanar da ficewa daga APC ne a wurin wani taro tare da magoya bayansa wanda ya gudana a Otal ɗin Haske Luxury, Minna, babban birnin Neja ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng