Shugaban APC da ya gina jam'iyyar a Neja ya fice daga cikin jam'iyyar mai mulki

Shugaban APC da ya gina jam'iyyar a Neja ya fice daga cikin jam'iyyar mai mulki

  • Shugaban APC na farko tun bayan kafa jam'iyyar a Neja, Alhaji Bako Shettima, ya tattara kayansa ya yi murabus daga cikinta
  • Shettima wanda ke neman takarar gwamnan a Neja, ya ce jam'iyyar ta cika kudin Fom kuma hakan ya nuna ba dan mutane aka kafa ta ba
  • Haka nan ya faɗa wa dumbin magoya bayansa cewa yana nan kan bakarsa ta neman gwamna, zai faɗi jam'iyyar da zasu koma nan gaba

Niger - Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC tun farkon kafa ta reshen jihar Neja, Alhaji Bako Shettima, ya fice daga jam'iyya mai mulki.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon jigo a APC ya bayyana dalilinsa na ɗaukar wannan matakin da wasu abubuwa da ake yi a jam'iyyar da suka sha ƙarfinsa.

Tambarin jam'iyyar APC.
Shugaban APC da ya gina jam'iyyar a Neja ya fice daga cikin jam'iyyar mai mulki Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Shettima wanda ke fafutukar zama gwamnan Neja ya sanar da ficewa daga APC ne a wurin wani taro tare da magoya bayansa wanda ya gudana a Otal ɗin Haske Luxury, Minna, babban birnin Neja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Sai dai fitaccen ɗan siyasan ya kauce wa magana game da jam'iyyar siyasan da zai koma bayan barin APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa ya ɗauki matakin barin APC?

Ɗan takarar gwamnan ya ƙara da cewa APC ta nuna a zahiri cewa kuɗi ta sanya a gaba fiye da mutanen da ke cikinsa, misali shi ne makudan kuɗin da ta zabga wa Fom ɗin takara.

Shettima ya aike da tambaya kai tsaye da cewa:

"Jam'iyyar da take ikirarin cewa ta mutane ce kuma ta tafi kai tsaye ta zarce dukkan sauran jam'iyyu wajen karɓan makudan kudi wurin yan Najeriya, Shin jam'iyyar tana nufin hana mutane shiga zabe ne?"
"Duba da wannan lamarin na yanke hukuncin watsar da kokarin cika burina a ƙarƙashin APC. Zan bayyana inda muka dosa ga masoya na yan Neja nan da yan kwanaki."

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Sai dai ya ƙara jaddada cewa fita daga APC ba yana nufin ya jingine burinsa na zama gwamna ba, wata hanya ce ta shirywa yaƙi ba dan fita yaƙi ba.

A wani labarin kuma Jam'iyya mai mulki ta yi babban kamu, Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC a Oyo

Sanata mai wakiltar mazaɓar Oyo ta kudu, Sanata Kola Balogun, ya koma jam'iyyar APC ranar Laraba bayan ficewa daga PDP.

Sanatan, wanda ɗan uwa ne ga babban Sarkin ƙasar Ibadan, Oba Lekan Balogun, ya ɗauki matakin ne don yin ta zarce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262