Jam'iyyar mai mulki ta yi babban kamu, Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC a Oyo

Jam'iyyar mai mulki ta yi babban kamu, Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC a Oyo

  • Sanata mai wakiltar mazaɓar Oyo ta kudu, Sanata Kola Balogun, ya koma jam'iyyar APC ranar Laraba bayan ficewa daga PDP
  • Sanatan, wanda ɗan uwa ne ga babban Sarkin ƙasar Ibadan, Oba Lekan Balogun, ya ɗauki matakin ne don yin ta zarce
  • Haka nan a ranar Asabar da ta shuɗe, wani ɗan majalisar wakilai a Oyo ya fice daga PDP kuma ya koma jam'iyyar APC

Oyo - Biyo bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP, Sanata mai wakiltar mazaɓar Oyo ta kudu, Sanata Kola Balogun, ya koma jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Ledearship ta rahoto cewa ɗan majalisar ya cimma matsaya ranar Laraba na shiga jam'iyyar hamayya a jihar Oyo, APC, domin samun tikitin zarcewa kan kujerarsa a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Sanata Kola Balogun
Jam'iyyar mai mulki ta yi babban kamu, Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC a Oyo Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Idan zaku iya tunawa Sanata Balogun, ƙani ga babban basaraken ƙasar Ibadan wanda ake kira Olubadan na Ibadan Land, Oba Lekan Balogun, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP ranar Litinin.

Ya ɗauki wannan matakin ne bayan gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya miƙa tikitin takarar Sanatan Oyo ta kudu ga Mogaji Joseph Tegbe, wanda ya sauya sheka daga APC ba da jimawa ba.

Haka nan a ranar Asabar, Honorabul Muraina Ajibola, wanda ke kan kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya karo na uku ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Bayan samun wannnan cigaban, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a halin yanzu ita ke da Sanatoci uku baki ɗaya da yan majalisar wakilai 11 cikin 14 a jihar Oyo.

Zaɓen 2023

A halin yanzun kowace jam'iyyar siyasa a Najeriya ta maida hankali wurin shiryawa domin tunkarar bababban zaɓen 2023 dake tafe.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Manyan jam'iyyu biyu da muke da su, PDP da APC na ta faɗi tashin kawo ƙarshen taƙaddama game da tsarin mulkin karɓa-karba.

Babu jam'iyya da ta yanke kai tikitin takarar shugaban ƙasa wani yanki, ana hasashen cewa zasu bar kofa a buɗe domin tsayar da wanda zai kawo musu nasara.

A wani labarin na daban kuma Wani Sanatan APC daga kudu ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun , ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Sanatan ya sanar da burinsa na zama shugaban ƙasa ne a wani taro da aka shirya a babban birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel