Bayan Amaechi, Ngige, Wani Ministan Buhari ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023

Bayan Amaechi, Ngige, Wani Ministan Buhari ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin APC
  • Mista Onu ya bayyana kansa da mutum mai tsantsar tausayi kuma wanda ya san matsalolin mutane da hanyar magance su
  • Ya kuma bayyana yadda a ƙarƙashinsa yan Najeriya musamman mata masu ciki ke samun kula da lafiya kyauta

Abuja - Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ayyana kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen 2023 dake tafe.

Onu ya shiga tseren kujera lamba ɗaya a Najeriya ne a wurin wani taro da aka shirya a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Tsohon gwamnan Abia, ya bayyana kansa da a matsayin, "Mutum mai matuƙar tausayi," inda ya ƙara da cewa a ƙarƙashinsa Najeriya ta fara samar da kula da lafiya kyauta a Asibitocin gwamnati.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu.
Bayan Amaechi, Ngige, Wani Ministan Buhari ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Bayan ɓangaren lafiya, Ministan ya ce jahar Abia ta ga cigaba ta kowane ɓangare a lokacin mulkinsa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

A jawabinsa, Ministan ya ce:

"A matsayin mutum mai tausayi, kuma wanda ya yi imanin cewa mata na da rawar takawa wajen gina ƙasa, bana son mace mai ciki ko jaririnta su mutu yayin ɗawainiya da juna biyu ko lokacin haihuwa."
"Wannan ne lokaci ma fi wahala a wurin mata saboda wasu ba su iya biyan kuɗin da za'a kula da su. A yanzu kowace mata tana samun kulawa kyauta a Asibitocin gwamnati."

Kasar mu na da gobe mai kyau - Onu

Bugu da ƙari, Mista Onu ya yi kira ga dukkanin yan Najeriya musamman matasa su sani cewa kasar nan ta na da gobe mai kyau.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

"Bai kamata mu bar wani abu ya sa mu rika cire tsammani da goben kasar mu ba. Allah ne ya halicce mu a cikin ƙasar nan. Yan uwana yan Najeriya makullan buɗe cigaban ƙasar mu na hannun mu."
"Waɗan nan makullan sune ilimin da zai habaka tatttalin arziki ta kimiyya da fasaha, saboda haka ba kasar da ta cigaba a zamanance ba tare da amfani da kimiyya da fasaha ba."

A wani labarin kuma Jam'iyya mai mulki ta yi babban kamu, Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC a Oyo

Sanata mai wakiltar mazaɓar Oyo ta kudu, Sanata Kola Balogun, ya koma jam'iyyar APC ranar Laraba bayan ficewa daga PDP.

Sanatan, wanda ɗan uwa ne ga babban Sarkin ƙasar Ibadan, Oba Lekan Balogun, ya ɗauki matakin ne don yin ta zarce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel