Saida fam din Shugaban kasa a N40m ya yi yawa, Mai neman takara ya maka PDP a kotu
- Barista Okey Uzoho ya yi karar PDP a wani kotu da ke zama a garin Abuja a kan kudin sayen fam
- Okey Uzoho ya ce yana da sha’awar tsayawa takara a PDP a zaben 2003, amma an lafta farashin fam
- ‘Dan siyasar yana ganin ya cika duk wasu sharuda aka sani a doka, amma kudi ya zama masa cikas
Abuja – Barista Okey Uzoho wanda yana cikin masu neman shiga takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya kai karar jam’iyyarsa ta PDP har gaban kotu.
Daily Trust ta ce Okey Uzoho yana karar cewa jam’iyyar PDP ta hana shi damar shiga zaben fitar da gwani domin ya zama ‘dan takarar shugaban kasa.
Uzoho yana cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP masu rajista a Najeriya, ya koka da cewa kudin sayen fam din sha’awar tsayawa takara da aka sa ya yi yawa.
Hukumar dillacin labarai ta rahoto Lauyan yana mai kuka da farashin N40m da jam’iyyar ta yanke.
An kai PDP da INEC kotu
Jaridar The Cable ta ce Uzoho ya shigar da kara mai lamba FCT/CV/144/2022 ne a babban kotun tarayya da ke Abuja, ya na kalubalantar jam’iyyar ta sa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baya ga jam’iyyar PDP, Uzoho ya hada da hukumar zabe na kasa watau INEC a wannan shari’a. Dole wadannan bangarorin biyu su kare kansu a kotun.
Kudi ya zama sharadin takara?
A cewar wanda ya shigar da karar, amfani da kudi a matsayin karin sharadin shiga takara ya ci karo da sashe na 84 (3) na kundin tsarin mulkin 1999.
Har ila yau, Uzoho yana ganin kudin da aka yanke zai ci karo da sashe na (4) na dokar zaben kasa na shekarar 2022, domin za a hana wasu iya takarar.
Lauyan da ya tsayawa Uzoho ya shaidawa kotu cewa abin takaici ne a hana shi cika burinsa na zama ‘dan takarar PDP a zaben 2023 a dalilin kudin fam.
Me dokar zabe ta ce?
Saboda farashin yankan fam, ‘dan siyasar bai iya cika sharudan da aka bada na neman zama ‘dan takara ba, domin ba zai iya biyan miliyoyin a banki ba.
Rahoton ya ce Lauyan ya na ikirarin ya cika duk wasu jerin sharudan da aka ambata a sashe na 137 na tsarin mulki a kan tsayawa takara a dokar kasa.
Lauyan da ya kai kara ya bukaci a biya shi N50m saboda asarar da aka jawo masa a dalilin hana shi takara. Ba a sa ranar da za a fara sauraron shari’ar ba.
An hana wasu takara a PDP
Jiya aka ji labari akwai wadanda aka yi waje da su tun a wajen tantance ‘yan takara a jam’iyyar PDP. Hakan ya na nufin ba za su shiga zaben tsaida gwani ba.
Kwamitin David Mark ya haramtawa mutane biyu neman tikitin takarar shugaban kasa. Nwachukwu Anakwenze na cikin wadanda aka hana takara.
Asali: Legit.ng