2023: Tsohon Abokin Takarar Buhari Ya Lale N100m Ya Siya Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC
- Adadin mutanen da ke neman gadon kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a babban zaben 2023 da ke tafe na karuwa
- Mai tsokaci kan siyasa kuma marubuci, Fasto Tunde Bakare, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu zai kaddamar da takararsa a hukumance
- Tuni da Bakare ya siya fom din sha'awar shiga takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar APC mai mulki a kasa kan N100
Abuja - Shugaban Cocin Citadel Global Community a Najeriya, Tunde Bakare, a ranar Alhamis, ya siya fom din sha'awa da takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC gabanin zaben 2023 a Abuja, Vanguard ta rahoto.
Hakazalila, Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie, ta sanar da siyan fom din takarar na Bakare cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar 5 ga watan Mayu.
A cikin rubutun da ke hade da hoto, an hangi Fasto Bakare a hoton rike da fom din takarar da ya siya kan Naira miliyan 100 na jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriya.
Ya shiga jerin yan takara masu yawa da ke neman samun tikitin takarar jam'iyyar mai mulki na APC da za ta yi zaben fidda gwani a ranar 30 ga watan Mayun 2022.
Fasto Bakare zai kaddamar da takarasa a hukumance cikin yan kwanaki
Sai dai, Legit.ng ta tattaro cewa Fasto Bakare zai yi taro a ranar 9 ga watan Mayu idan zai kaddamar da takararsa a hukumance.
An shirya yin taron ne a cibiyar Shehu Musa Yar'dua, Central Business District, Abuja da karfe 10 na safe.
Bakare ya zama mutum na goma sha 12 da ya siya fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC cikin wadanda suka shirin fafatawa da irin su mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Bola Ahmed Tinubu, Rotimi Amaechi da sauransu.
Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan
A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.
Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.
Asali: Legit.ng