Yanzu haka: Yan sanda sun kwace sakatariyar PDP a wata jahar kudu

Yanzu haka: Yan sanda sun kwace sakatariyar PDP a wata jahar kudu

  • Jami'an yan sanda dauke da makamai sun mamaye sakatariyar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Abia
  • Hakazalika sun hana ma'aikata da bakin da suka ziyarci sakatariyar a safiyar yau Alhamis, 5 ga watan Mayu, shiga harabar
  • Sai dai kuma, kakakin jam'iyyar a jihar ya bayyana cewa an baiwa ma'aikatan hutun kwana daya ne domin su je gida su huta

Abia - Jami’an yan sanda a safiyar ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, sun karbe sakatariyar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Abia.

Jami’an tsaron wadanda ke dauke da makamai sun hana ma’aikata da baki shiga harabar sakatariyar wacce ke a unguwar Finbars, Umuahia.

Daya daga cikinsu da aka tuntuba ya ce umurni ne daga sama, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Yanzu haka: Yan sanda sun kwace sakatariya PDP a wata jahar kudu
Yanzu haka: Yan sanda sun kwace sakatariya PDP a wata jahar kudu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Da aka tuntube shi, sakataren labarai na PDP, Hon. Fabian Nwankwo, ya ce ba abun tayar da hankali bane.

Ya ce jam’iyyar na hutun kwana daya ne sannan ya bukaci jami’an jam’iyyar da ma’aikata da su zauna a gida su huta, rahoton Punch.

A cewarsa jami’an jam’iyyar da ma’aikata na bukatar hutu saboda gajiyan da suka tara daga ayyukan da suka sha na tsawon makonni.

Ya bayyana cewa harkoki za su dawo a sakatariyar gobe, yana mai cewa kasancewar jami’an tsaro a harabar ba sabon abu bane.

Tun a ranar Talata ake ta zanga-zanga a sakatariyar sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar kan taron wakilan jam’iyyar guda uku.

Wasu mutane sun zargi bangaren Dr Asiforo Okere da ke shugabancin jam’iyyar a jihar da hada kai da kuma yin kulla-kulla domin juya tsarin don daura wani dan takarar gwamna da suke so.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Sun nemi ya gaggauta yin murabus ko a tsige shi domin ba jam’iyyar damar samun shugaba da zai ba dukkanin yan takara damar fafatawa.

Amma an yi zanga-zangar adawa da hakan a ranar Laraba yayin da dimbin jama’a suka kewaye ofishin domin nuna goyon baya ga shugabancin Okere.

Sun bukace shi da kada ya ji tsoron wadanda ke yunkurin kwace mulki.

Kwamitin Ayyuka na Jihar mai mambobi 47, ya kuma kori wadanda suka yi zanga-zangar da korafi kan shugaban.

APC ta tsawaita wa'adin sayar da fom din takara na 2023

A wani labaria na daban, jam'iyyar APC ta sanar da tsawaita wa'adin sayar da fom din takara na zaben 2023 mai zuwa zuwa 10 ga watan Mayun bana.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar ke ci gaba da samun masu tsayawa takara daga bangarori daban-daban na kasar nan, musamman na kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga shafin APC na Twitter ne ya bayyana sauyin jadawalin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng