An gano su wanene mutum 2 da Jam’iyyar PDP ta haramtawa neman takarar Shugaban kasa

An gano su wanene mutum 2 da Jam’iyyar PDP ta haramtawa neman takarar Shugaban kasa

  • Wadanda aka yi waje da su tun a wajen tantance ‘yan takara a jam’iyyar PDP ba za su shiga zabe ba
  • Kwamitin David Mark ya haramtawa mutane biyu neman tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Uwar jam’iyya ta amince da matakin da kwamitin ya zartar, alhali masu neman takara sun saye fam

Abuja - A ranar Laraba, 4 ga watan Mayu 2022, jam’iyyar PDP ta tabbatar da matakin da kwamitin tantance masu neman takarar shugaban kasa ya dauka.

Rahoton Daily Trust ya ce shugaban jam’iyya na kasa, Iyorchia Ayu ya amince da aikin kwamitin.

Kwamitin David Mark ya tantance duka mutane 17 da suke neman tikitin shugaban kasa a karkashin PDP, a karshe ‘yan siyasa biyu ne ba su sha ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wadanda aka hana neman takarar a jam’iyyar hamayyar su ne Dr. Nwachukwu Anakwenze da kuma Hon. Cosmas Ndukwe.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Kwamitin na David Mark mai dauke da mutane 9 bai yi wa ‘yan jarida bayanin dalilin haramtawa wadannan ‘yan siyasa shiga zaben fitar da gwani a 2023 ba.

Haka zalika uwar jam’iyyar ba tayi karin haske a kan dalilin daukar wannan mataki mai tsauri ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

PDP presidential screening appeal panel
Shugaban PDP na kasa tare da Atiku Abubakar Hoto: @Big_daddy33
Asali: Twitter

Meyasa aka hana su takara?

Abin da aka sani shi ne masu son takara a 2023 ba su cika sharudan harin kujerar shugaban kasa ba. Ragowar mutanen da aka tantance, sun cika sharudan.

Legit.ng Hausa ta na zargin hana Hon. Ndukwe damar shiga zaben tsaida ‘dan takara bayan ya biya kudin fam bai rasa nasaba da karar da ya kai PDP a kotu.

Ndukwe ya hakikance a kan cewa a zabe mai zuwa na 2023, dole ne a ba mutanen Kudu maso gabas damar shugabancin Najeriya, har ya kai kara kan hakan.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Menene laifin Nwachukwu Anakwenze?

Shi ma Nwachukwu Anakwenze ya yi asarar kudin da ya biya na fam domin ba zai yi takara ba. Anakwenze yana ikirarin shi ya cancanta a ba tikiti a 2023.

Kamar dai Ndukwe, Dr. Anakwenze yana ganin Ibo ya cancanta ya rike mulkin kasar nan. Kungiyar ASAW da yake jagoranta ta dade da wannan burin.

Ndume bai tare da Arewa

An ji Mohammed Ali Ndume, Sanata mai wakiltar kudancin Borno a majalisar dattawa, yana cewa sai Arewa ta fi amfana idan har mulki ya koma kudu.

Sanatan ya ce adalci da gaskiya shi ne ya zama wanda zai karbi mulki daga hannun Muhammadu Buhari ya zama mutumin Kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng