Gwamnan APC a Arewa da wani Ministan Buhari sun ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
- Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya, Abubakar Badaru, ya sayi Fom din tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
- Ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya bi sahun gwamnan ya tara masoya ya bayyana kudirinsa idan ya zama shugaban kasa
- Manyan jiga-jigan siyasar biyu sun shiga tseren ne karkashin inuwar jam'iyya mai mulki wato APC
Abuja - Gwamnan Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru, da ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, sun ayyana kudirinsu na tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin APC.
Gwamna Badaru ya sayi Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara a Hedkwatar APC ta ƙasa dake Abuja ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da farko dai an fara alaƙanta Badaru da neman takarar kujerar Sanata a zaɓe mai zuwa, amma rahoto ya nuna ya canza aniyarsa bayan gana wa da masu ruwa da tsaki na APC a fadar gwamnati ranar Talata da dare.
Duk da babu wani cikakken dalilin canza ra'ayi, amma bayani sun nuna gwamnan ya sha fama da matsin lamba daga takwarorinsa na ya nemi takarar shugaban ƙasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mashawarcin gwamnan na musamman kan harkokin Midiya, Habibu Nuhu Kila, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce:
"Dagaske ne gwamna Badaru ya garzaya Abuja domin ya Sayi Fom din nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa."
Yace idan aka ba gwamnan damar zama magajin Buhari zai cigaba da kyawawan shirye-shirye da tsarukan da shugaban ya kafa.
Akpabio ya shiga tseren takara a 2023
A nasa bangaren, Akpabio ya sha alwashin ba zai bar Najeriya ta yi tangal-tangal ba, inda ya ƙara da cewa zai dawo da martaba, girma, mutuncin ƙasa ga yan Najeriya.
Da yake jawabi a gaban daruruwan masoya ranar Laraba yayin ayyana shiga takara a filin Ikot Ekpene Township, tsohon gwamnan ya ce zai kawo ɗaukakar da mutanen Akwa Ibom suka gani a matakin ƙasa.
Ya ce:
"Kun ji ayyana shiga takara da dama amma wannan ba kamar saura take ba, ba sakon sa rai bane kaɗai, sako ne na dawo da martaba girma da mutuncin Najeriya a yankin Afirka da sassan duniya."
"Ina bukatar kuri'un ku na zama shugaban ƙasa a 2023, ina godiya ga shugaban ƙasa bisa damar da ya bani na yi aiki gaba da jihar Akwa Ibom. Shugaban yana yakar cin hanci yadda nike fata."
A wani labarin kuma Gwamnan APC ya yabi ɗan takarar shugaban ƙasan PDP, ya ce yana alfahari da shi
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Ƙatsina ya yabi takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, kan matakin da ya ɗauka game da IPOB.
Gwamnan ya ce ba zai taɓa mancewa da goyon bayan da mutan Ribas suka ba shi ba lokacin yana kakakin majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng