Zamfara: Kwamishina Ya Yi Murabus Don Gudun Kada a Tsige Shi Daga Kujerarsa Kan Wa'azin Da Ya Yi

Zamfara: Kwamishina Ya Yi Murabus Don Gudun Kada a Tsige Shi Daga Kujerarsa Kan Wa'azin Da Ya Yi

  • Kwamishinan harkokin addini na Jihar Zamfara, Tukur Jangebe, ya yi murabus daga kujerarsa bayan ya fahimci ana yunkurin tsige shi
  • Ana zargin kwamishinan da yawan kambama abokan hamayyar gwamman Jihar Zamfara yayin wa’azozinsa na watan Ramadan
  • Wani ma kusa da gwamnatin ya bayyana wa manema labarai cewa ya samu kishin-kishin akan shirin tsige shi bayan shagalin Idi, hakan yasa ya yi murabus

Zamfara - Tukur Jangebe, Kwamishinan harkokin addini na Jihar Zamfara ya yi murabus daga mukaminsa bayan ya gano ina shirin tsige shi daga kujerarsa akan yanayin wa’azinsa da wasu kusoshi su ke dauka a matsayin suka ga gwamnatin jihar.

Ana zargin Kwamishinan, wanda sannen malami mai wa’azi ne da yaba wa abokan hamayyar gwamnan yayin da ya ke wa’azi a watan Ramadan, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya faɗi matakin da gwamnatinsa zata ɗauka kan duk ɗan takarar da yaƙi yin murabus

Zamfara: Kwamishina Ya Yi Murabus Don Gudun Kada a Tsige Shi Daga Kujerarsa Kan Wa'azin Da Ya Yi
Kwamishina a Zamfara Ya Yi Murabus Don Gudun Kada a Tsige Shi Daga Kujerarsa Kan Wa'azin Da Ya Yi. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Wani babban mai mukami a gwamnatin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya sanar da Premium Times cewa malamin ya samu labarin shirin tozarta shi ta hanyar tube shi daga madafun iko bayan shagalin Idi, hakan ya sa ya yi saurin murabus kafin lokacin.

Jangebe ya tabbatar da murabus din

Yayin da Premium Times ta bukaci tattaunawa da Jangebe ta wayar salula, ya ce ya yi murabus amma bai fadada bayanin ba.

Kamar yadda ya shaida:

"Eh, na yi murabus daga gwamnatin. Na tura takardar murabus ranar 1 ga watan Mayun 2022. Za ku iya rubuta wannan. Ubangiji ya saukaka mana.”

Abin da takardar ta kunsa

A takardar wacce ta yadu a kafafen sada zumunta, Jangebe ya yi godiya ga gwamnan jihar, Bello Muhammad da ya ba shi damar yi wa jihar aikii. Amma bai bayyana dalilinsa na murabus ba.

Kara karanta wannan

Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu jiga-jigan FG su yi murabus

Zailani Bappa, hadimin gwamnan na harkar yada labarai, ya ce ya ga wasikar amma gwamnatin jihar ba ta riga ta zauna ba akanta.

Ya ci gaba da cewa:

“Ban ji muryarsa a gidan rediyo ba ya na tabbatar da murabus din nashi ba, don haka a matsayin jita-jita na dauki labarin.”

Sai dai sakataren watsa labaran gwamnan, wanda yanzu sakataren watsa labaran jam’iyyar APC ne na jihar, Yusuf Idris, ya ce kwamishinan ya yi murabus ne don ya tsaya takara a shekarar 2023.

Zamfara: Kwamishina Ya Yi Murabus Don Gudun Kada a Tsige Shi Daga Kujerarsa Kan Wa'azin Da Ya Yi
Takardan Murabus Din Kwamishina a Zamfara. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

An koka akan yadda kwamishinan ya ke kambama abokan hamayyar gwamnan da yi musu addu’o’in nasara

Amma wata majiya daga hadimin gwamnan na sama-sama ta ce gwamnati ta hassala da irin wa’azin kwamishinan.

Majiyar ta shaida yadda wasu hadiman gwamnan a shekarar 2021 su ka koka akan yadda Jangebe ya ke kin amfani da damar wa’azinsa wurin kambama gwamnan ga masu zuwa wa’azi.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Ya ci gaba da cewa bai dace a bar shi a kujerar ba musamman ganin yadda a duk wa’azinsa ya ke yi wa abokan hamayyar gwamnan addu’o’in fatan alheri tare da caccakar gwamnatin da ya ke aiki a karkashinta.

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel