2023: Bidiyon Ziyarar Da Wike Ya Kai Wa Mahaifiyar Marigayi Ƴar'Adua a Katsina
- Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya kai wa mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua, Hajia Aya Dada Yar’Adua ziyara a Katsina
- Wike yanzu haka dan takarar shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar PDP kuma ya kai mata ziyara ne tare da tsohon Gwamna Ibrahim Shema ranar Talata
- Ya kai ziyarar ne yayin da ake shirye-shiryen yin zaben fidda gwanin jam’iyyar inda ya gaisa da ita da harshen Turanci yayin da Shema ya ke fassara mata
Katsina - Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Ribas, ya kai ziyara ga mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua, Hajia Aya Dada Yar’Adua a Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Wike dan takarar shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar PDP, kuma ya kai ziyara ne a ranar Talata tare da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yar’Adua ya rasu ne yayin da ya ke kan karagar mulki shekaru 12 da su ka gabata.
Ya kai ziyarar ne yayin da zaben fidda gwanin PDP ya ke karatowa
Wike ya kai ziyarar ne don samun damar ganawa da wakilan jam’iyyar PDP yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa kamar yadda Daily Trust ta nuna.
A wani bidiyo na sakwanni 25, an ga Wike ya na gaisawa da mahaifiyar Yar’Adua inda ya yi mata sallama sannan ta amsa.
Mahaifiyar Yar’Adua ta yi godiya ga Gwamnan Ribas din da harshen Hausa inda Shema ya ke fassara ma Wike, bisa ziyarar da ya kai mata.
Ga bidiyon a kasa:
Wike ya gana da Masari
Bayan isarsu gidan Gwamnatin Muhammadu Buhari da ke Katsina, Wike ya je har wurin Masari domin sanar da shi kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 inda ya nemi goyon bayansa.
Masari ya bukaci duk wasu ‘yan siyasar kasar nan da su kasance masu zage damtse wurin ganin ci gaban kasa idan ba haka ba kowa zai wahala.
Masari ya yaba wa Wike akan babbar rawar da ya taka wurin dakatar da IPOB daga bulla Jihar Ribas, inda ya kara da cewa hakan ya tallafa wa siyasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng