Labari da duminsa: APC ta tsawaita wa'adin sayar da fom din takara na 2023
- Yayin da 'yan siyasa ke ci gaba da sayen fom din takara na kujeru daban-daban gabanin zaben fidda gwani, APC ta fitar da sabuwar sanarwa
- Jaam'iyyar ta bayyana cewa, ta sake duba jadawalin ayyukanta, ta kuma dage wa'adin sayar da foma-foman takara
- Hakazalika, sauyin ya shafi jadawalin mayar da cikakken fom din da 'yan siyasa suka saya zuwa wani lokaci
Jam'iyyar APC ta sanar da tsawaita wa'adin sayar da fom din takara na zaben 2023 mai zuwa zuwa 10 ga watan Mayun bana.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar ke ci gaba da samun masu tsayawa takara daga bangarori daban-daban na kasar nan, musamman na kujerar shugaban kasa.
Wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga shafin APC na Twitter ne ya bayyana sauyin jadawalin.
A cewar wani bangare na rubutun:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A cikin jaddawalin da aka sake ingantawa, yanzu an mayar da ranar karshe na mayar da da fom da takaddu zuwa ranar Laraba, 11 ga Mayu.
"Majalisar Wakilai za ta zabi wakilai na Kananan Hukumomi, Jihohi da na Kasa a ranar 12 zuwa 14 ga Mayu"
Tsohon shugaban APC ya bayyana aniyarsa ta gaje kujerar Buhari
A ranar Laraba ne tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa Adams Oshiomhole ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, The Nation ta ruwaito.
Da yake bayyana aniyarsa a cibiyar fasaha da al’adu ta Cyprian Ekwensi Abuja, tsohon gwamnan na Edo ya ce ya shiga jerin wadanda za su fafata ne don canza kanun labarai ga daukacin ‘yan Najeriya.
Oshiomole ya bayyana aniyarsa ne jim kadan bayan da ya karyata jita-jitar yana da sha'awar tsayawa takara a zaben 2023.
Ya zuwa yanzu dai jiga-jigai daga APC na ci gaba da nuna sha'awarsu ga dane kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wacce hawanta ya nuna sai mai sa'a.
2023: 'Yan APC a yankin Yarbawa za su zauna, su hada kai su zabi mai gaje Buhari daga yankinsu
A wani labarin na daban, shugabanin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Yamma za su gana da masu neman takarar shugaban kasa na yankin a ranar Juma’a a jihar Legas, kamar yadda jaridar WesternPost ta ruwaito.
An bayyana cewa taron zai gudana ne a gidan gwamnatin Legas.
Rahoton da Legit.ng Hausa ke samu daga TheCable ya bayyana cewa Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC ne zai jagoranci taron.
Asali: Legit.ng