Hotuna: Tinubu ya ziyarci shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja
- Jigon jam'iyyar APC kuma dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar, Bola Tinubu, ya ziyarci Shugaba Buhari
- Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Buhari a ranar Talata bayan dawowarsa daga Makka yin aikin Umra
- Tinubu yana daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC da aka gayyata buda-baki a ranar 26 ga Afirilu amma bai samu halarta ba saboda yana Makka
Aso Villa, Abuja - A daren Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakuncin tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban cin kasa, Bola Ahmed Tinubu, a gidansa da ke fadar shugaban kasa a Abuja.
An sakankance cewa taron da suka yi cigaba ne na tattaunawa da suka fara a matsayinsu na jiga-jigan jam'iyyar.
An tattaro cewa, Tinubu bai samu halartar liyafar buda-bakin da aka shirya saboda shugabannin jam'iyyar APC ba saboda ya je Makka yin Umra.
Dan takarar shugabancin kasa yana daga cikin jerin mutum 18 wadanda suka kasance jiga-jigan APC kuma aka gayyace su buda-baki a fadar shugaban kasa a ranar 26 ga watan Afirilu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A lokacin rubuta wannan rahoton, babu cikakken bayani kan abinda suka tattauna yayin taron.
Asali: Legit.ng