Dan takarar gwamna tare da ɗaruruwan mambobin APC sun fice daga jam'iyyar a Kwara

Dan takarar gwamna tare da ɗaruruwan mambobin APC sun fice daga jam'iyyar a Kwara

  • Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Kwara, Hakeem Lawal, ya tabbatar da ficewarsa daga APC, ya koma SDP
  • Alhaji Hakeem Lawal, ɗaya ɗaga cikin 'ya'yan tsohon gwamna Muhammed Lawal, ya ce ya yi shawari kafin ɗaukar matakin
  • Har yanzun rikicin APC a jihar Kwara ƙara gaba yake kuma masana siyasa na hangen jam'iyyar na iya samun babbar matsala

Kwara - Tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Kwara, Alhaji Hakeem Lawan, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar SDP a hukumance.

Alhaji Lawal, wanda ɗaya ne daga cikin 'ya'yan marigayi tsohon gwamnan jihar, Alhaji Muhammad Lawal, ya yi takarar gwamna karkashin APC a zaɓen 2019.

Fitaccen ɗan siyasan ya tabbatar da sauya shekarsa daga APC zuwa SDP a hukumance ne a mahaifarsa Idi Ape ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, kamar yaɗda This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Sabon ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayyana aniyarsa a APC, ya nemi a rage masa kuɗin Fom

Alhaji Hakeem Lawal.
Dan takarar gwamna tare da ɗaruruwan mambobin APC sun fice daga jam'iyyar a Kwara Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Tribune Online ta ruwaito cewa Alhaji Hakeem Lawal ya jagoranci dandazon magoya bayansa da masu masa fatan Alheri zuwa jam'iyyar SDP.

Meyasa ya zaɓi komawa SDP?

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala rijista da SDP, Lawal ya ce:

"Na kawo ziyara asalina ne domin na gaida yan uwana. Kyakkyawan tarban da na samu daga dattawa, mata da matasa ita ce soyayya ta gaskiya, ina fatan Allah ya bani ikon saka muku irin wanan soyayya da kuke mun."
"Na yi shawara mai zurfi a ciki da wajen kananan hukumomi 16, masalahar da na gano ita ce jam'iyyar SDP ce ta fi dacewa da mu, tawagar mu da kuma cika burin mu da kudirin mu ga jihar mu."
"Saboda haka na saurari kiran ku kuma na yi rijistar zama mamba a SDP reshen jihar Kwara. Na samu rakiyar shugaban SDP na Ilorin ta gabas tare da wasu mambobinsa, da kuma shugabannin gundumomi 12 a Ilorin ta gabas."

Kara karanta wannan

Bayan Yahaya Bello, wani gwamnan APC ya lale Miliyan N100m ya sayi Fom ɗin takarar shugaban kasa na APC

Biyo bayan faruwar haka, masana siyasa sun yi hasashen cewa rikicin da yaƙi karewa a APC ta jihar Kwara ka iya jawo mata asarar wani babban jigo nan gaba.

A wani labarin kuma Sanata Stella Oduah ta fice daga jam'iyyar APC, ta koma tsagin hamayya PDP

Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta arewa, Sanata Stella Oduah, ta tabbatar da sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.

Sanatar wacce tana ɗaya daga cikin masu kai kudiri, ta ɗauki wannan matakin ne bayan zaman shawari da jiga-jigan PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel