Da Dumi-Dumi: An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takarar PDP suka fara dira Sakatariya

Da Dumi-Dumi: An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takarar PDP suka fara dira Sakatariya

  • Jami'an tsaro sun mamaye Sakatariyar PDP dake Patakwal a jihar Ribas yayin da ake gab da fara tantance yan takara
  • Yan sanda, DSS da sauran jami'an tsaro sun hana kowa shiga har sai ka gabatar da katin shaida ko da ɗan jarida ne kafin ka shiga
  • Tuni dai yan takarar gwamna a zaɓe mai zuwa daga jihohin ƙasar nan suka fara isa wurin da za'a tantance su a cikin Sakatariyar

Rivers - An ƙara tsaurara tsaro a Sakatariyar shiyya ta jam'iyyar PDP dake Patakwal, yayin da ake shirye-shiryen fara tantance yan takarar gwamna.

Yan takara daga jihohin Bayelsa, Akwa Ibom, Delta, Kuros Riba da Edo tuni suka dira wurin tantancewar wanda ke a Sakatariyar shiyya dake kan hanyar Aba, Patakwal.

Kara karanta wannan

2023: Tsoffin ministocin PDP sun cimma matsaya kan yadda za su fatattaki APC

Jam'iyyar PDP.
Da Dumi-Dumi: An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takarar PDP suka fara dira Sakatariya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto cewa an yi ruwan dakarun tsaro a wurin, wanda ya haɗa da dakarun yan sanda, DSS, da sauran su.

Bayanai sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun hana kowa shiga yayin da suke tambayar katin shaida kafin ko ɗan jarida ne su bashi damar shiga wurin.

Wane yan takara ne suka fara dira wurin?

Wasu daga cikin yan takarar gwamna a babban zaɓe mai zuwa da aka ga zuwan su wurin tantancewar sun haɗa da tsohon shugaban PDP na jiha, Felix Obuah, da kuma Sanata Lee Maeba.

Sauran jiga-jigan yan takara da aka hanga sun isa wurin sune; tsohon ministan Sufuri, Dakta Abiye Sekibo, da David Briggs da dai sauran yan takara.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa bayan rikicin da ya auku jiya wurin tantancewa, Gwamna Wike na jihar Ribas ya shelanta neman ɗan majalisar tarayya ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Hotunan 'Dawafi na musamman da aka yi don Tinubu a Masallacin Harami, yace a yiwa Najeriya addu'a

Gwamnan ya zargi ɗan majalisar kuma ɗan takarar gwamnan da ɗakko hayar yan daba domin su ta da zaune tsaye, su hana cigaban aikin.

A wani labarin kuma Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari, zai lale miliyan N100m ƙuɗin Fom

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Dimeji Bankole, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Wani makusancin Bankole ya tabbatar da cewa Uban gidansa ya fara shirye-shirye, kuma zai karɓi Fom mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262